Yanzu-Yanzu: Ƙungiyar CAN Za Ta Yi Gagarumin Zanga-Zanga Na Ƙasa Kan Kisar Deborah Samuel

Yanzu-Yanzu: Ƙungiyar CAN Za Ta Yi Gagarumin Zanga-Zanga Na Ƙasa Kan Kisar Deborah Samuel

  • Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta umurci mambobinta a kasa su shirya yin zanga-zangar lumana a ranar Lahadi 22 ga watan Mayun 2022
  • CAN za ta yi wannan zanga-zangar ne domin nuna kin amincewarsu da kisar Deborah Samuel a Sokoto wacce matasa suka kan batanci ga Annabi (SAW)
  • Sanarwar ta CAN ta ce za a yi zanga-zangar ne a haraban sakatariyar CAN a jihohin Najeriya ba kan tituna ba domin kada a sake rasa rayyuka

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta bukaci a yi zanga-zanga na kasa bisa kisar da aka yi wa Deborah Samuel, dalibar aji 2 na Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, rahoton Vanguard.

Shugaban CAN, Rabaran Olasupo Ayokunle, cikin wasikar da ya aike wa dukkan shugabannin kungiyar, ya bukaci kiristoci su yi zanga-zangar lumana a harabar cocinsu a ranar Lahadi 22 ga watan Mayun 2022.

Kara karanta wannan

Zagin Annabi a Sokoto: Masu zanga-zanga sun farmaka tare da lalata coci 2 a Sokoto

Yanzu-Yanzu: Ƙungiyar CAN Ta Buƙaci A Yi Zanga-Zanga a Ƙasa Kan Kisar Deborah Samuel
'Kungiyar CAN Ta Buƙaci A Yi Zanga-Zanga a Ƙasa Kan Kisar Deborah Samuel. Hoto: Vanguard.

Ya yi kirar ne bayan kisa da kona wata daliba da fusatattun matasa suka yi bayan zarginta da furta kalaman batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

Wasikar mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Mayun 2022 dauke da sa hannun sakatare janar na CAN, Joseph Daramola, ta ce:

"Shugaban CAN, mai alfarma Rabaran Dr Samson Olasupo A. Ayokunle ya umurci ni da in sanar da dukkan shugabannin coci, su shirya zanga-zangar lumana don karramar yar mu, Deborah Yakubu wacce aka kashe a ranar Alhamis 12 ga watan Mayun 2022 a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari a Sokoto Jihar Sokoto."

A harabar coci za a yi zanga-zangar ba a tituna ba - CAN

Za a yi zanga-zangan ne a ranar 22 ga watan Mayun 2022 da karfe 3 na rana a dukkan sakatariyar CAN a kasa ba kan tituna ba domin kiyaye rasu rayyuka. Wadanda ba su da sakatariyar CAN suna iya amfani da kowanne haraban babban coci.

Kara karanta wannan

Dokar kulle: Bishop Kukah ya yabawa matakin Tambuwal, ya karyata batun kai hari gidansa

"Za mu rike takardu dauke da sakonni kamar "Muna neman a yi wa Deborah Adalci,"A dena kisa da sunan Ubangiji" "Ya isa haka" "Yan sanda, ku dakatar da kisa ba dalili a Najeriya" "Kirista dai-dai suke da kowa a kasar nan" "Dole a hukunta wadanda suka kashe Deborah" "Muna Alla wadai da kisa saboda addini" "Ba mu amince da musulmi masu tsatsauran ra'ayi ba".

Sakon ta cigaba da cewa wadanda suke da hali su yi amfani da kafafen watsa labarai na dandalin sada zumunta don sanar da duniya abin da ke faruwa.

An kuma yi kira ga kiristoci da ke wasu kasashen duniya su yi zanga-zangar a rassan cocin a kasashen su.

"Ana kuma iya amfani da taron don yin addu'a ga iyalan Deborah da abokanta, da kuma neman zaman lafiya a kasa da shugabanni da babban zabe da ke tafe."

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

Kara karanta wannan

Sokoto: Mutane sun mamaye tituna da zanga-zanga, sun nemi a saki waɗan da suka kashe ɗalibar da ta zagi Annabi

A wani rahoton, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ya nisanta kansa daga yin ala-wadai akan kisan Deborah Samuel.

Deborah dalibar aji biyu ce a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto, kuma kirista ce, an halaka ta ne bisa zarginta da yin batanci ga Annabi Muhammad SAW.

Sai dai Atiku ya yi wata wallafa a Twitter inda ya ce:

“Babu adalci dangane da kisan muguntar da aka yi mata. An halaka Deborah Yakubu kuma wajibi ne a kwatar mata hakkinta akan wadanda su ka halaka ta. Ina mai yi wa ‘yan uwanta da kawayenta ta’aziyya.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel