Shekara da mutuwar Shekau: Waiwaye ga hare-haren Boko Haram 12 da suka girgiza duniya

Shekara da mutuwar Shekau: Waiwaye ga hare-haren Boko Haram 12 da suka girgiza duniya

A yau ne shugaban 'yan ta'addan Boko Haram Abubakar Shekau ke cika shekara guda da barin duniya, tun bayan da rahotanni suka ce ya sheke kansa a wani artabu da 'yan uwansa 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan ISWAP ne.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Boko Haram dai kungiya ce ta ta'addanci da ta shahara a Najeriya da kasashen nahiyar Afrika makwabta, inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma salwantar dukiyoyi da ababen more rayuwa.

An san kungiyar da kai hare-hare kan ababen gwamnati, daidaikun jama'a har ma da wuraren ibada da makarantu.

Shekakken shugaban 'yan ta'adda Shekau
Shekara 1 da mutuwar Shekau: Waiwaye ga hare-haren Boko Haram 12 da suka girgiza duniya | Hoto: saharareporters.com
Asali: Twitter

A yayin da Shekau ke cika shekara guda a ksa, mun kawo muku jerin hare-haren da ya alakanta kansa da su kuma suka ja hankalin duniya.

1. Harin hedkwatar 'yan sanda ta Abuja - 16 ga watan Yunin 2011

Kara karanta wannan

Kaduna: Rayuka 3 sun salwanta, miyagu sun sace mutum 9 a sabon farmaki

Kungiyar ta Boko Haram, ta ce ta kai harin bam din da aka kai ranar Alhamis 16 ga watan Yuni a hedikwatar 'yan sandan Najeriya wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla shida.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

'Yan sandan sun ce daya daga cikin wadanda suka mutu dan kunar bakin wake ne, wanda shi ne harin farko da ya fara girgiza kasar nan, kamar yadda BBC News ta ruwaito.

2. Harin ofishin majalisar dinkin duniya - 26 ga watan Agustan 2011

A ranar 26 ga watan Agustan 2011 ne Boko Haram ta sake kai mummunan harin nakiya ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke babban birnin Najeriya, inji rahoton Guardian.

Akalla mutane 20 ne suka mutu a harin, wanda sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon, ya bayyana a matsayin "kai hari kan wadanda suka dukufa wajen taimakon wasu".

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ministar kudi ta dakatar da Akanta-Janar na tarayya don bincike kan badakalar naira biliyan 80

3. Hare-haren Jos, Gadaka, Damaturu da Suleja - 25 ga watan Disamban 2011

Boko Haram sun kai jerin hare-hare a lokacin bukukuwan Kirsimeti a Arewacin Najeriya a ranar 25 ga Disamba 2011.

An samu tashin bama-bamai da harbe-harbe a coci-coci a Madalla, Jos, Gadaka, da Damaturu. An rahoto cewa, akalla mutane 41 ne suka mutu.

Daga baya kungiyar Boko Haram, ta dauki alhakin kai hare-haren, kamar yadda US Today ta tattaro.

4. Harin Boko Haram a jihar Kano - 20 ga watan Janairun 2012

'Yan Boko Haram sun kai mummunan hari a birnin Kano, inda akalla mutane 178 suka mutu, kamar yadda jaridar Reuters ta ruwaito.

Kamar dai kullum, an ta'allaka wannan mummunan harin da ya yi sanadiyyar asara da yawa kan kungiyar Boko Haram da ke kara kamari a lokacin.

5. Kisan kiyashin Baga - 16 ga watan Afrilun 2012

Kara karanta wannan

Hanyar Abuja-Kaduna: A jiya Talata kadai, mutum 20 sun kone kurmus a hadarin mota, yan bindiga sun sace 30

A ranar 16 ga watan Afrilun 2013 ne Boko Haram suka kai harin kisan kiyashi a garin Baga a kauyen Baga da ke jihar Borno, inda suka kashe fararen hula kusan 200 tare da raunata daruruwa, gami da lalata gidaje da kasuwanni sama da 2,000 na miliyoyin Naira.

'Yan gudun hijira, jami'an farar hula, da kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun zargi sojojin Najeriya da aikata kisan kiyashi; yayin da wasu jami’an soji suka dora laifin a kan kungiyar ta Boko Haram, inji rahoton New York Times.

6. Mummunan harin Buni Yadi kan daliban sakandare - 25 Fabrairun 2014

A ranar 25 ga Fabrairu, 2014 ne Shekau ya umarni kai hari kan daliban sakandaren Buni Yadi a jihar Yobe, an kashe yara maza 59 a kwalejin, inji Guardian.

An kuma kona gine-gine ashirin da hudu na makarantar a sakamakon harin.

Duk da cewa babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma a cewar kafafen yada labarai da dama da jami'an tsaron Najeriya ana kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka kai harin.

Kara karanta wannan

Batanci: Ku girmama addinin mutane da abinda suka yi imani da shi sai a zauna lafiya, El-Rufa'i

7. Harin Nyanya - 14 ga watan Afrilun 2014

A ranar 14 ga Afrilu, 2014 da misalin karfe 6:45 na safe, wasu bama-bamai biyu sun tashi a tashar motar Nyanya a jihar Nasarawa, inda mutane akalla 71 suka mutu tare da raunata akalla 200, in ji wani rahoton The Wall Street Journal.

Tashar motar dai na da tazarar kilomita 8 ne da Kudu maso Yammacin babban birnin tarayya Abuja.

Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai harin kwanaki shida bayan faruwarSA. Hakan ya faru ne 'yan sa'o'i kadan kafin sace daliban Chibok.

8. Sace daliban Chibok - 15 ga watan Afrilun 2014

A daren ranar 14-15 ga Afrilu, 2014, Boko Haram ta sace dalibai mata 276 yawancinsu 'yan tsakanin shekaru 16 zuwa 18 daga makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno.

Kafin kai farmakin dai an rufe makarantar na tsawon makonni hudu saboda tabarbarewar yanayin tsaro, amma ‘yan matan sun hallara a ranar da aka sace su domin yin jarabawar karshe a fannin 'Physics', inji rahoton Small War Journal.

Kara karanta wannan

Sokoto: An ayyana neman wadanda aka gani a bidiyon kone dalibar da ta zagi Annabi

Wannan hari dai ya jawo hankalin kungoyiyi da dama a duniya, inda ake kira ga kara kaimin gwamnati kan harkokin tsaro.

9. Mummunan harin Bama - 2 ga watan Satumban 2014

Kungiyar Boko Haram ta kwace garin Bama a jihar Borno, lamarin da ya sa sojoji suka musanta rahotannin da ke cewa gwamnati na iya rasa iko da yankin Arewa maso Gabas, kamar yadda Al-Jazeera ta ruwaito.

Rahotanni da dama sun bayyana yadda harin ya kai ga mutuwar mutane da yawa a yankin tare da barin mutum sama da duba 20 a matsayin 'yan gudun hijira bayan kwace garin.

Mazauna garin Bama da wani dan siyasa a yankin sun fada a ranar Talata cewa dakaru 400 wadanda wasunsu ba su da makamai ko takalmi, sun gudu bayan da wani jirgin soji ya yi kuskuren farmakar barikin garin.

10. Harin masallacin Juma'a a Kano - 28 ga watan Nuwamban 2014

Kara karanta wannan

Al’ummar gari sun tsere cikin jeji yayin da yan bindiga suka farmaki garuruwan Neja

A ranar 28 ga watan Nuwamba, 2014, Boko Haram suka kai mummunan hari a babban masallacin Juma'a na Kano, birni mafi girma a Arewacin Najeriya.

Masallacin yana kusa da fadar Sarkin Kano na wancan lokacin, Muhammad Sanusi II, wanda ya bukaci jama'a da su kare kansu ta hanyar daukar makamai domin yakar 'yan Boko Haram.

Wasu ‘yan kunar bakin wake biyu ne suka tarwatsa kansu inda wasu da bindiga suka bude wuta kan wadanda ke kokarin tserewa, kamar yadda AlJazeera ta ruwaito.

Kimanin mutane 120 ne suka mutu sannan wasu 260 suka jikkata. An ta'allaka harin ga kungiyar Boko Haram.

11. Harin Madagali - 9 ga watan Disamban 2016

An kai harin kunar bakin wake a Madagali a ranar 9 ga watan Disambar 2016 lokacin da wasu mata biyu suka ta da bama-bamai biyu a garin na Madagali ta jihar Adamawa.

Harin ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 57 tare da jikkata 177. Daga cikin wadanda suka jikkata 120 an ruwaito cewa yara ne. Jami’ai sun dora laifin a kan ‘yan kungiyar Boko Haram, kamar yadda NBC News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Deborah Samuel: Ƴan Najeriya Sun Yi Wa Ɗan Tsohon IGP Martani Kan Kalamansa Game Da Kisar Ɗalibar Sokoto Da Ta Zagi Annabi

12. Kisan manoman shinkafa a Borno - 28 ga watan Nuwamban 2020

Mayakan Boko Haram sun kashe akalla manoma 43 tare da raunata 6 a gonakin shinkafa da ke kusa da birnin Maiduguri a ranar Asabar 28 ga watan Nuwamban 2020.

Maharan sun daure manoman ne tare da yanke makogwaronsu a kauyen Koshobe, in ji wani rahoton The Guardian.

ISWAP Sun Afkawa Mafakar Boko Haram, Ana Kyautata Zaton Shekau Ya Mutu

A wani labarin, wasu da ake zargin 'yan ISWAP ne a ranar Laraba sun kashe shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, yayin wani kazamin fada a maboyar su ta Dajin Sambisa.

In ji wata majiya da ba a tabbatar ba, Vanguard ta ruwaito. Gandun dajin Sambisa yana da iyaka da kananan hukumomin Konduga, Bama, Gwoza Askira Uba, Hawul, Kaga da Biu a kananan hukumomin Borno, tare da wasu yankuna na Gujuba, Buni Yadi, Goniri a Yobe da Madagali a jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

An ji labarin mutuwar Fasto, makonni 8 bayan ‘Yan garkuwa da mutane sun dauke shi

Wasu majiyoyi sun ce daruruwan mayakan ISWAP sun mamaye Sambisa da motoci dauke da manyan bindigogi da ke farautar Shekau wanda shi ne shugaban kungiyar Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.