Yanzu Yanzu: Ministar kudi ta dakatar da Akanta-Janar na tarayya don bincike kan badakalar naira biliyan 80

Yanzu Yanzu: Ministar kudi ta dakatar da Akanta-Janar na tarayya don bincike kan badakalar naira biliyan 80

  • Zainab Ahmed, ministar kudi ta kasa ta dakatar da Akanta Janar na tarayya, Idris Ahmed, har sai baba-ta-gani
  • An dauki wannan matakin ne domin bayar da damar bincike a tsanaki kan zargin da ake masa na almundahana da karkatar da kudin gwamnati
  • A tsawon lokacin da dakatarwar zai yi aiki, an ce ba a bukatarsa a ofis kuma ba a bukatar ya tuntubi wani jami'i a ofishin nasa

Abuja - Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed, ta dakatar da babban akanta-janar na tarayya, Ahmed Idris, har sai baba-ta-gani.

Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kama shi kan zargin wawure kudi naira biliyan 80, jaridar The Cable ta rahoto.

Yanzu Yanzu: Ministar kudi ta dakatar da Akanta-Janar na tarayya don bincike kan badakalar naira biliyan 80
Yanzu Yanzu: Ministar kudi ta dakatar da Akanta-Janar na tarayya don bincike kan badakalar naira biliyan 80 Hoto: Thisday
Asali: UGC

A wata wasika mai kwanan wata 18 ga watan Mayu, 2022, Ahmed ta ce dakatarwar ‘ba tare da biya ba’ ya kasance ne domin bayar da damar yin bincike a tsanaki ba tare da cikas ba daidai da dokokin aikin gwamnati.

Kara karanta wannan

Rashawar N80bn: EFCC ta sauya wa Akanta-Janar wurin zama daga Kano inda aka kama shi

Ba a bukatar ya zo ofis ko kuma ya tuntubi kowani jami’I a ofishinsa sai dai don wani zama na ladabtarwa wanda za a iya bayar da shawara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An Kama Akanta-Janar Na Tarayyar Najeriya, Ahmed Idris

A baya mun kawo cewa an samu sahihin rahoto da ke tabbatar da cewa an kama Akanta Janar na tarayyar Najeriya, Ahmed Idris, kan zargin almundahanar kudi da karkatar da kudin gwamnati.

Wadanda suke da masaniya kan lamarin sun ce jami'an EFCC na Kano ne suka kama Idris a yammacin ranar Litinin kuma za a tafi da shi Abuja domin amsa tambayoyi.

Majiyoyi sun ce EFCC ta dade tana bincike a kan zargin karkatar da Naira biliyan 80 na kudin gwamnati ta hanyar wasu kwangiloli na bogi.

Masu binciken sun ce an gano cewar kamfanonin da aka yi amfani da su wurin karkatar da kudin suna da alaka da yan uwan Akant Janar din da abokansa.

Kara karanta wannan

Sokoto: An ayyana neman wadanda aka gani a bidiyon kone dalibar da ta zagi Annabi

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng