Kaduna: Rayuka 3 sun salwanta, miyagu sun sace mutum 9 a sabon farmaki

Kaduna: Rayuka 3 sun salwanta, miyagu sun sace mutum 9 a sabon farmaki

  • Miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki yankin Tokace da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna
  • Mazaunin yankin ya sanar da cewa 'yan bindigan sun bayyana da yawansu wurin karfe 9 na dare kuma suka dinga harbi
  • Wurin gudun ceton rai ne miyagun suka harbe wasu mutum uku yayin da suka yi garkuwa da wasu mutum tara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Chikun, Kaduna - Mutum uku aka gano sun rasa rayukansu yayin da wasu tara aka sace su a sabon farmaki da 'yan bindiga suka kai wa al'ummar Tokace da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

A wata tattaunawa waya da TheCable, wani mazaunin yankin wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce an kai farmakin wurin karfe 9 na daren Talata.

Kaduna: Rayuka 3 sun salwanta, miyagu sun sace mutum 9 a sabon farmaki
Kaduna: Rayuka 3 sun salwanta, miyagu sun sace mutum 9 a sabon farmaki. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ya ce 'yan bindigan da suka bayyana da yawansu sun dinga harbi babu kakkautawa kuma yayin da mazauna yankin ke gudun ceton rai, an halaka mutum uku.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: ‘Yan bindiga sun kashe 3 a dangin shugaban karamar hukuma da mai gadi

"'Yan bindigan sun iso wurin karfe 9 na dare kuma suka fara harbe-harbe. Duk mun tsorata kuma kowa ya fara gudu zuwa daji domin tseratar da rayuwarsa," yace.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"An halaka mutum uku yayin da suke neman tsira. Sun sace mutum tara."

Wannan farmakin na zuwa ne bayan sa'o'i kadan da 'yan ta'adda suka sace mutane a kan babban titin Abuja zuwa Kaduna.

Sama da tubabbun 'yan ta'adda 51,000 da iyalansu ke hannunmu, Rundunar sojin Najeriya

A wani labari na daban, fiye da tubabbun 'yan ta'adda 51,000 da iyalansu ne suka zub da makamansu ga sojojin yankin Arewa maso Gabas kamar yadda sojojin suka bayyana.

Kwamandan rundunar operation Hadin Kai, Manjo Janar Chris Musa, ya bayyana wa Channels TV yayin tattaunawar da suka yi da shi a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna

Ya bayyana yadda mazauna yankin suka dinga taimakon sojoji, musamman yadda suka samu bayanan sirri duk da cewa akwai bangaren da aka sanya wa shamakin sadarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel