Da Dumi-Dumi: ISWAP Sun Afkawa Mafakar Boko Haram, Ana Kyautata Zaton Shekau Ya Mutu

Da Dumi-Dumi: ISWAP Sun Afkawa Mafakar Boko Haram, Ana Kyautata Zaton Shekau Ya Mutu

- Wasu rahotannin tsaoro sun ce an kashe shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau

- Rahoton ya ce kungiyar ISWAP ce ta afkawa mafakar kungiyar Boko Haram a wannan makon

- An ce, ISWAP ta ragargaza fadar Shekau tare da kwace mulkinsa wanda daga nan ya kashe kansa

Wasu da ake zargin 'yan ISWAP ne a ranar Laraba sun kashe shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, yayin wani kazamin fada a maboyar su ta Dajin Sambisa. In ji wata majiya da ba a tabbatar ba, Vanguard ta ruwaito.

Gandun dajin Sambisa yana da iyaka da kananan hukumomin Konduga, Bama, Gwoza Askira Uba, Hawul, Kaga da Biu a kananan hukumomin Borno, tare da wasu yankuna na Gujuba, Buni Yadi, Goniri a Yobe da Madagali a jihar Adamawa.

Wasu majiyoyi sun ce daruruwan mayakan ISWAP sun mamaye Sambisa da motoci dauke da manyan bindigogi da ke farautar Shekau wanda shi ne shugaban kungiyar Boko Haram.

KU KARANTA: A karon farko: ’Yan bindiga sun kai hari cikin garin Batsari da ke Katsina

Da Dumi-Dumi: ISWAP Sun Afkawa Mafakar Shekau, Ya Kashe Kansa da Kansa
Da Dumi-Dumi: ISWAP Sun Afkawa Mafakar Shekau, Ya Kashe Kansa da Kansa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Haka kuma an bayyana cewa ba kungiyar ISWAP ba ce ta kashe Shekau kai tsaye, ana zargin ya tarwatsa kansa ya kashe kansa ne a lokacin da ISWAP ta yi yunkurin cafke shi (Shekau) da ransa, a yayin musayar wuta.

Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance ko tabbaci kan mutuwar shugaban ‘yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo, jami’an tsaron Najeriya, mutane da yawa sun shiga dandalin su na sada zumunta na murnar mutuwar Shekau da safiyar Alhamis.

A cewar wani rahoton tsaro da aka samu ya ce, “majiyar da ba a tabbatar ba ta ruwaito cewa shugaban kungiyar JAS Abubakar shekau ISWAP ta hanbarar da mulkinsa kuma sun mamaye dajin sambisa baki daya.

“Tare da wadannan ci gaban ISWAP sun fi JAS kayan aiki da kudade. Don haka yanayin barnarsu zai canza, kuma akwai yiwuwar za a fuskanci hare-hare akai-akai a kewayen Konduga, Bama, Gwoza, Biu LGA’S da wani yanki na Adamawa.

"Duk 'yan Adam da ke kusa da wannan yankin su kasance masu lura da tsaro kuma su kasance masu sanya ido."

KU KARANTA: Wabba: El-Rufai Ya Yi Hayar 'Yan Daba Cike Da Manyan Motoci 50 Su Fatattaki NLC

A wani labarin, Jami'an rundunar 'yan sanda reshen jihar Benue sun kama wasu mutane 131 da ake zargi da aikata laifi a fadin jihar. Ana zarginsu da aikata laifuka da suka hada da satar mutane, fashi da makami da kuma barna ta kungiyar asiri.

‘Yan sanda sun kuma kwato makamai daban-daban guda 785 daga hannun su. Wannan ya kasance ne kamar yadda rundunar ta kuma bai wa jami'anta guda bakwai, wadanda suka yi fice a fagen ayyukansu kyautuka na kwarai.

Wannan karimcin, a cewar kwamishinan 'yan sanda (CP) Audu Madaki, shi ne karfafa jami'an rundunar su kara himma a bangarorinsu daban-daban na kokarin dakile ta'addanci a jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel