Hukumar Soji ta ƙaddamar da atisayen rugurguza ɓarayin shanu
Hukumar sojin Najeriya karkashin jagorancin rundunar ta jihar Kaduna, ta ƙaddamar da wani sabon atisaye na musamman domin kawo ƙarshen rikicin satar shanu a wasu sassa na jihohin Kaduna da Neja.
Da sanadin jaridar The Punch, Legit.ng ta fahimci cewa, wannan sabon atisaye da aka yiwa laƙabin 'Ƙaramin Goro' zai ƙunshin hadin gwiwar jami'ai na hukumomin 'yan sanda da kuma na fararen kaya wato DSS, sai kuma hukumar jami'ai masu jar kwala ta NSCDC tare da hukumar sojin sama.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne, mataimakin kakakin hukumar sojin ƙasan Najeriya, Kanal Muhammad Dole ya bayyana hakan, inda ya ce yawaitar ta'addaci da suka hadar da fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu da makamantansu ne ya sanya hukumar ta ƙaddamar da wannan atisaye.
Dole yake cewa, duk da wannan atisaye da zasu gudanar a yankunan, hakan ba zai janyo tsaiko ko muzugunawa al'umma ba, domin kuwa sun shirye-shirye na kaucewa assasa jerin gwanon motoci akan manyan hanyoyi.
KARANTA KUMA: Jam'iyyar APGA ta amince da shugaba Buhari
Mataimakin kakakin sojin ya kuma nemi taimako tare da hadin gwiwar daukacin al'ummar ƙasar nan wajen samar da rahotanni da zasu tallafa musu wajen samun nasarar wanzar da zaman lafiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng