Rashawar N80bn: EFCC ta sauya wa Akanta-Janar wurin zama daga Kano inda aka kama shi

Rashawar N80bn: EFCC ta sauya wa Akanta-Janar wurin zama daga Kano inda aka kama shi

  • An sauyawa Akanta-Janar na Tarayya Ahmed Idris, wanda ke hannun EFCC bisa zargin zamba wurin zama, an mayar da shi Abuja
  • Majiyoyin da suka zanta da ‘yan jarida sun yi ikirarin cewa hukumar ta kuma gayyaci ‘yan uwan Idris a ci gaba da bincike
  • Manufar, kamar yadda EFCC ta yi ikirari, ita ce a kusantar da wadanda ake zargin zuwa inda aka aikata galibin laifuka kafin a kama su

Abuja - Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ta sauya wa babban Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris wurin zama; daga Kano zuwa Abuja.

Wasu majiyoyi a hukumar sun shaidawa jaridar The Nation a ranar Talata, 17 ga watan Mayu, cewa an gayyaci ‘yan uwan Idris da ta ta hanyarsu ya aiwatar da zambar da ake tsare da shi akai domin yi masa tambayoyi sosai.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ministar kudi ta dakatar da Akanta-Janar na tarayya don bincike kan badakalar naira biliyan 80

Akanta-Janar ya bar Kano zuwa Abuja a hannun EFCC
Rashawar N80bn: EFCC ta sauya wa Akanta-Janar wurin zama daga Kano inda aka kama shi | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Daya daga cikin majiyar ta shaida wa jaridar cewa:

“Hukumar ta dauke AG-F daga Kano zuwa Abuja domin yi masa tambayoyi. Tuni ya fara ba jami'an binciken mu hadin kai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ya zuwa yanzu dai yana tsare ne saboda EFCC ta gayyaci wasu daga cikin ‘yan uwansa da kuma mashawartansa wadanda ake zargin sun aiwatar da wasu kwangiloli da ake zargin babu su.
"Hukumar za ta yi wa al'ummar kasa bayanin yadda ya kamata bayan binciken mu."

An tattaro cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kai Idris Abuja inda ya aikata mafi yawan laifukan da ake zarginsa da aikatawa, domin a gudanar da bincike mai inganci, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

An Kama Akanta-Janar Na Tarayyar Najeriya, Ahmed Idris

A tun farko a makon nan, jaridar Premium Times ta ce ta samu sahihin rahoto da ke tabbatar da cewa an kama Akanta Janar na tarayyar Najeriya, Ahmed Idris, kan zargin almundahanar kudi da karkatar da kudin gwamnati.

Kara karanta wannan

Hanyar Abuja-Kaduna: A jiya Talata kadai, mutum 20 sun kone kurmus a hadarin mota, yan bindiga sun sace 30

Wadanda suke da masaniya kan lamarin sun ce jami'an EFCC na Kano ne suka kama Idris a yammacin ranar Litinin kuma za a tafi da shi Abuja domin amsa tambayoyi.

Majiyoyi sun ce EFCC ta dade tana bincike a kan zargin karkatar da Naira biliyan 80 na kudin gwamnati ta hanyar wasu kwangiloli na bogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel