Ku share ASUU ku koma aji: Shawarin gwamnan APC ga lakcarorin da ke yajin aiki

Ku share ASUU ku koma aji: Shawarin gwamnan APC ga lakcarorin da ke yajin aiki

  • Gwamnan jihar Yobe ya shawarci malaman jami'a da su koma ayyukansu su yi watsi da kungiyarsu ta ASUU
  • Gwamnan ya ce, gwamnatinsa bata taba tauye hakkin malamin jami'a ba, don haka bai kamata yajin ya shafe ta ba
  • Idan baku manta ba, malaman jami'a karkashin ASUU na ci gaba da zaman yajin aiki na tsawon lokaci a Najeriya

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi kira ga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta jami’ar jihar Yobe da su sake duba matsayar su kan yajin aikin da kungiyar ta kasa ke ci gaba da yi.

Buni, wanda ya gana da mahukuntan makarantar da kungiyar, ya ce gwamnatin jihar da jami’ar ba su da wata matsala a tsakaninsu, don haka babu hujjar rufe jami'ar, inji rahoton Premium Times.

Malaman jami'o'i sun shafe fiye da watanni biyu suna yajin aiki saboda neman ingantacciyar walwala da kayan aiki don habaka sana'arsu ta koyarwa.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Rokon gwamna Buni ga malaman jami'a
Ku share ASUU ku koma aji: Shawarin gwamnan APC ga lakcarorin da ke yajin aiki | Hoto: leadership.ng
Asali: Facebook

Gwamnan wanda sakataren gwamnatin jihar Baba Malam Wali ya wakilta a wurin taron, ya kuma yi kira ga malaman da su yi la’akari da halin da daliban da yajin aikin ya shafe ke ciki, inji rahoton Daily Post.

A cewarsa:

“Mun kira wannan taron ne domin mu yi kira gare ku, da mahukuntan jami’ar, da kungiyoyin kwadago da ku sake duba matakin da kuka dauka a baya na shiga yajin aikin da kungiyar ta kasa ta fara a fadin kasar nan da sunan hadin kai."

Gwamnatin Yobe bata taba kuntatawa lakcarori ba

Ya kara da cewa gwamnatin jihar Yobe ba ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na jami'ar.

Ya kuma ce ya kamata malamai su yi la’akari da tallafi/hannun jarin da gwamnati ta zuba a jami’ar.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Buni ya ce baya ga saka hannun jarin manyan ayyuka a cibiyar, gwamnatinsa na biyan albashi da alawus-alawus na malamai cikin gaggawa.

Mataimakin shugaban jami’ar Mala Daura da shugaban kungiyar ASUU Mohammed Jajare sun godewa gwamnatin jiha bisa tallafin da take baiwa jami’ar tare da yin alkawarin cewa mambobin kungiyar za su hadu domin duba koken gwamnati kuma za su tuntube ta.

Dalibai sun shiga tasku, ASUU ta tsawaita yajin aikinta da karin watanni 3

A wani labarin, kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta tsawaita yajin aikin da take yi da makwanni goma sha biyu, kamar yadda shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana a ranar Litinin, inji majiyar gidan talabijin na Channels.

Wannan na zuwa ne bayan da dalibai da iyayensu ke ci gaba da jiran karshen yajin aikin da ya barke a shekarar nan.

A wata sanarwa da ya fitar bayan taron malaman jama'o'i da aka gudanar a Jami’ar Abuja, shugaban ASUU ya ce sun yanke shawarar baiwa gwamnati isasshen lokaci domin warware duk wasu matsaloli da malaman ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Asali: Legit.ng

Online view pixel