Dalibai sun shiga tasku, ASUU ta tsawaita yajin aikinta da karin watanni 3

Dalibai sun shiga tasku, ASUU ta tsawaita yajin aikinta da karin watanni 3

  • Bayan dogon shawari da kuma kai ruwa rana, ASUU ta sake tsawaita yajin aikin da take yi zuwa akalla makwanni 12
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da iyaye da dalibai ke ci gaba da jiran lokacin da kungiyar zata kawo karshen yajin aikin
  • Wata sanarwar da shugaban ASUU ya fitar ta bayyana dalilin da yasa kungiyar ta yanke shawarar tsawaita yajin aikin

Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta tsawaita yajin aikin da take yi da makwanni goma sha biyu, kamar yadda shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana a ranar Litinin, inji majiyar gidan talabijin na Channels.

Wannan na zuwa ne bayan da dalibai da iyayensu ke ci gaba da jiran karshen yajin aikin da ya barke a shekarar nan.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Yajin aikin ASUU na kara tabarbarewa
Labari da dumi-dumi: ASUU ta tsawaita yajin aikinta da karin watanni 3 | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A wata sanarwa da ya fitar bayan taron malaman jama'o'i da aka gudanar a Jami’ar Abuja, shugaban ASUU ya ce sun yanke shawarar baiwa gwamnati isasshen lokaci domin warware duk wasu matsaloli da malaman ke fuskanta.

Sanarwar ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Bayan tattaunawa mai zurfi, lura da gazawar gwamnati wajen sauke nauyin da ke kanta tare da gaggauta magance duk wasu batutuwan da aka bijiro dasu a cikin takardar yarjejeniyar FG/ASUU ta 2020 (MoA) a cikin karin mako takwas na yajin aikin da aka ayyana a ranar 14 ga Maris 2022, NEC ta yanke shawarar tsawaita yajin aikin na tsawon makwanni goma sha biyu domin baiwa Gwamnati karin lokaci domin shawo kan matsalolin da suka addabe su cikin gamsuwa.”

Yajin aikin zai fara ne daga karfe 12:01 na daren ranar Litinin, 9 ga Mayu, 2022, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

Majalisar zartarwa ta ASUU na tattaunawa, ta yuwu a kara wa'adin yajin aiki

A wani labarin, mambobin majalisar zartarwa ta Kungiyar Malamai masu Koyarwa ta Jami'o'in Najeriya a halin yanzu sun shiga ganawa, jaridar Punch ta gano hakan.

Wani mamban majalisar zartarwar ya sanarwa da Punch cewa ta yuwu a kara wa'adin yajin aikin duba da abinda ake tattaunawa a cikin taron yanzu.

A ranar 14 ga watan Fabrairun 2022, Kungiyar Malamai masu Koyarwa ta jami'o'in Najeriya suka shiga yajin aikin jan kunne domin assasa biyan wasu bukatunsa daga gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel