ASUU: Daliban Najeriya A Shirye Suke A Bindige Su Don Kawo Karshen Yajin Aiki, Shugaban NANS

ASUU: Daliban Najeriya A Shirye Suke A Bindige Su Don Kawo Karshen Yajin Aiki, Shugaban NANS

  • Kungiyar Daliban Jami'o'in Najeriya, NANS, ta ce mambobinta a shirye suke a bindige su domin kawo karshen yajin aiki kungiyar ASUU
  • Mr Sunday Asefon, Shugaban NANS na kasa ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a Channels Television game da yajin aikin ASUU
  • Asefon ya ce bisa ga alamu gwamnati ta fi mayar da hankali kan zabe ne ba batun ilimi ba don haka za su fita zanga-zanga idan kuma an harbe su zai zama sadaukarwa amma ba za su cigaba da zuba ido ba

Shugaban Kungiyar Daliban Najeriya na Kasa, NANS, Sunday Asefon, a ranar Alhamis, ya ce kungiyar a shirye ta ke fita titi ta yi zanga-zanga kan yajin aikin da kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, ke yi.

Mr Asefon ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke magana a shirin Sunrise Daily na Channels Television.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu

ASUU: Daliban Najeriya A Shirye Suke A Bindige Su Don Kawo Karshen Yajin Aiki, Shugaban NANS
ASUU: Daliban Najeriya A Shirye Suke A Bindige Su Don Kawo Karshen Yajin Aiki, In Ji Shugaban NANS. Hoto: Daily Trust.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Mr Asefon, babu alamun cewa gwamnatin tana da shirin kawo karshen yajin aikin duba da ta mayar da hankali kan zaben shekarar 2023.

Ya yi misali da yajin aikin da wasu daliban jami'o'i suka yi a Benin-City.

"Muna magana kan ilimi ne, muna magana kan rayuwa," in ji shi.
"Shugabannin mu ba su tattauna rayuwarmu, shugabannin da muka zaba; amma sun mayar da hankalinsu kan zabe ne. Suna maganan zaben ne saboda son kansu da bukatunsu.
"Mun shirya yaki, iya abin da za su iya yi shine su harbe mu," in ji shi.
"Idan sunyi harbi, za su fada wa yan sanda su harbe mu, idan mun mutu, wadanda za su zo a bayan mu za su san cewa mun mutu wurin yaki domin su. Za ku su san cewa an harbe mu ne don suna shirin zabe. Amma dole mu dauki mataki."

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Mr Asefon ya ce gwamnati ta dena yin siyasa da batun ASUU.

Yajin Aikin ASUU: Jami'ar Jihar Kaduna Ta Umurci Ɗalibai Da Malamai Su Koma Makaranta Bayan Sallah

A wani rahoton, mahukunta a Jami'ar Jihar Kaduna, KASU, sun shirya fara zangon karatu na 2020/2021 a ranar 9 ga watan Mayu, Channels TV ta rahoto.

Jami'ar, cikin sanarwar da ta fitar mai dauke da kwanan watan 26 ga watan Afrilu da sa hannun sakataren harkokin karatu, Abdullahi Zubairu, ta umurci dalibai da malaman makarantar su cigaba da karatu.

Sanarwar ta kuma shawarci dukkan malamai da daliban jami'ar su yi biyayya ga tsarin karatun makarantar kamar yadda Information Nigeria ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel