Yajin Aikin ASUU: Jami'ar Jihar Kaduna Ta Umurci Ɗalibai Da Malamai Su Koma Makaranta Bayan Sallah

Yajin Aikin ASUU: Jami'ar Jihar Kaduna Ta Umurci Ɗalibai Da Malamai Su Koma Makaranta Bayan Sallah

  • Jami'ar Jihar Kaduna, KASU, ta umurci dukkan dalibai da malamanta su dawo makaranta a ranar 9 ga watan Mayu
  • Hakan na kunshe ne cikin wata takarda da sakataren jami'ar, Abdullahi Zubairu ya fitar mai dauke da kwanan watar 26 ga watan Afrilu
  • Hakan na zuwa ne yayin da kungiyar malaman jami'o'i na kasa, ASUU, ke cigaba da yajin aikinta da ya kai kimanin watanni biyu yanzu

Kaduna - A yayin da kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, ke cigaba da yajin aiki, mahukunta a Jami'ar Jihar Kaduna, KASU, sun shirya fara zangon karatu na 2020/2021 a ranar 9 ga watan Mayu, Channels TV ta rahoto.

Jami'ar, cikin sanarwar da ta fitar mai dauke da kwanan watan 26 ga watan Afrilu da sa hannun sakataren harkokin karatu, Abdullahi Zubairu, ta umurci dalibai da malaman makarantar su cigaba da karatu.

Kara karanta wannan

Eid-el-Fitr: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranaku 2 na hutun Sallah

Yajin Aikin ASUU: Jami'ar Jihar Kaduna Ta Umurci Ɗalibai Da Malamai Su Koma Makaranta Bayan Sallah
Yajin Aikin ASUU: KASU Ta Umurci Ɗalibai Da Malamai Su Koma Makaranta Bayan Sallah. Hoto: Channels TV.
Asali: UGC

Sanarwar ta kuma shawarci dukkan malamai da daliban jami'ar su yi biyayya ga tsarin karatun makarantar kamar yadda Information Nigeria ta rahoto.

Yajin Aikin ASUU: Jami'ar Jihar Kaduna Ta Umurci Ɗalibai Da Malamai Su Koma Makaranta Bayan Sallah
Takardar Sanarwar komawa makaranta a ranar 9 ga watan Mayu a KASU. Hoto: KASU
Asali: Twitter

Yajin aikin na ASUU ya shiga wata na biyu kuma har yanzu ba a daidaita ba tsakanin gwamnatin tarayya da malaman.

Daliban Najeriya da dama sun sha nuna damuwarsu kan yajin aikin a dandalin sada zumunta.

ASUU ce kadai za ta iya janye yajin aiki, Ngige

A makon da ta gabata, Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige, ya ce ASUU ce kadai za ta iya janye yajin aikin tunda ita ce ta dauki matakin.

Wasu daga cikin bukatun na ASUU sun hada da neman a fitar da kudaden yin ayyukan inganta jami'o'i, sake duba yarjejeniyar FGN/ASUU ta 2009, biyan allawus din malaman jami'a da amfani da tsarin UTAS wurin biyan albashi da allawus din malaman jami'a.

Kara karanta wannan

Eid al Fitr: Hukumomin kasar Saudiyya sun sanar da ranar da za fara duban jinjirin watan sallah

Abin da wasu dalibai na Jami'ar Kaduna suka ce game da sanarwar komawa makaranta bayan sallah

Legit.ng Hausa ta samu ji ta bakin wasu dalibai na Jami'ar ta KASU inda suka tofa albarkacin bakinsu game da sanarwar ta jami'ar a fitar na cewa su dawo makaranta a ranar 9 ag watan Mayu.

Aminu Saeed, dalibi na ajin karshe Geography Department ya ce sun yi farin ciki da batun yana mai cewa dama sun dab da fara jarrabawa aka tafi yajin aikin.

"Muna maraba da sanarwar ta koma wa makaranta, dama jarrabawa muke shirin yi sai aka tafi yajin aikin, muna son mu koma makaranta mu kammala jarrabawa a sallame mu," in ji Aminu.

A bangarensa, Abdullahi Auwal wanda shima ajin karshe ya ke a Physics Department shima ya yi murna da batun koma wa makarantar.

"Ni gaskiya dama na gaji da zama a gida, na yi farin cikin ganin sanarwar bude makaranta bayan sallah, za mu kasance cikin shiri kuma muna godiya ga gwamnatin Kaduna da hukumar makaranta," in ji shi.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ƴan Siyasan Najeriya Sun Fi Boko Haram Hatsari, In Ji SSANU

Abdullahi Surajo da ke Geophysics Department dan aji daya shima ya magantu. Ya ce ya kosa a bude makarantar domin su fara karatu. Ya kuma yi fatan suma sauran makarantu a samu maslaha su koma.

"Dama na kosa a koma makaranta, ina fatana sauran makarantu suma nan bada dadewa ba a bude su koma," a cewarsa.

Ku Ba Mu N200m Cikin Kuɗin Tallafin Man Fetur, Mu Koma Aji: ASUU Ta Roƙi Gwamnatin Buhari

A wani rahoton, Shugaban Kungiyar malaman jami’o’i masu koyarwa, ASUU, Farfesa Emmanuel Osedeke ya ce gwamnatin tarayya har yanzu tana nuna halin ko-in-kula akan yajin aikin ASUU wanda hakan ya sa daliban jami’o’in Gwamnatin Najeriya suke zaune a gidajensu, rahoton The Punch.

A cewarsa, gwamnati ta kawo mafita akan kudin tallafin man fetur da kasafin Naira tiriliyan 4 amma kuma har yanzu bata ce komai ba akan ilimin jami’o’inta.

Farfesa Osodeke ya ce Naira biliyan 200 gwamnati za ta cire daga kudin kasafin tallafin man fetur, Naira Tiriliyan 4, sannan ta samu rarar Naira Tiriliyan 3.8 wurin kawo karshen matsalolin jami’o’i, Channels Television ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel