Group Admin ya yi 'batan dabo da N1.8m da mambobi suka hada a WhatsApp

Group Admin ya yi 'batan dabo da N1.8m da mambobi suka hada a WhatsApp

  • Wasu tsaffin daliban makaranta sun bude Whatsapp group inda suka tara kudi N1.8m don gyara makarantar da suka yi karatu
  • Amma an samu mishkila yayinda Admin ya yi awon gaba da kudin, ya koma kasar Birtaniya da zama
  • Yan Najeriya sun ofa albarkatun bakinsu kan wannan Admin da abinda yayi

Wani group Admin a manhajar WhatsApp ya yi 'batan dabo da kudin kungiyar tsaffin dalibai da suka tara don gyara makarantarsu ta sakandare.

Duk da ba'a bayyana sunan mutumin ba, labarin ya nuna cewa ya yi amfani da kudin wajen hada bizansa na komawa kasar Birtaniya.

Group Admin
Group Admin ya yi 'batan dabo da N1.8m da mambobi suka hada a WhatsApp Hoto: Aaron Foster, Jeffbergen and Chesnot (Ba ainihin hoton mutumin bane)
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace su bashi lokaci ya dawo musu da kudinsu

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro a kasar Saudi Arabia sun damke mabarata a Masjid Al-Haram

Wani shahrarren malamin Najeriya, Dipo Awojide, ya bada labarin a shafinsa na Tuwita.

Dipo Awojide yace mutumin yanzu yana bada hakuri kuma ya bukaci a bashi lokaci don ya tara kudin ya maida musu.

Yace:

"Kungiyar tsaffin daliban makarantar sakandare a WhatsApp sun hada N1.8m don gyara makarantarsu. Amma Admin ya yi amfani da kudin wajen guduwa Birtaniya tun Nuwamban 2021."
"Yanzu yana rokon a bashi lokaci ya dawo da kudin."

Kalli jawabinsa:

Tsokacin yan Najeriya:

Idris Nasidi Zango yace:

"Allah Shi kara
Da marayu may be akace a Tarawa kudin da baza'a Tara haka ba. Amma da yake Dinner ce za'a hade kowa ya bayar."

Abdullahi Katsina Muhammad:

Kuma da za'ayi addu'ar "Allah ya tsinewa maciya amanar qasar nan" Admin din nan fa na iya cewa Ameeen

Sheikh AK Bin Ahmad:

"Kaci banza baba
Kai a hakan ma qaramin barawo ne, wasu anaji ana gani suke sunqumawa a aljihunsu amma ba’a ce komai ba."

Kara karanta wannan

Magidanci ya cika bujensa da iska bayan matarsa ta haifa ƴan huɗu

Salis Pantami yace:

"Gaskiya na karanta comments din mutane da yawa amma qalilanne masu hankali aciki
Taya za'a tara kudi don gyaran makaranta don kannesu suji dadin karatu, wani a gudu da kudin dan hauka amma kana goyon bayan sa kamar wani abun burge wa yayi
Gaskiya Yakamata mu chanza halinmu wlh
Bai kanata muna goyon bayan barna bau."

Asali: Legit.ng

Online view pixel