Da dumi-dumi: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci

Da dumi-dumi: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Abdulganiyu Jaji a matsayin sabon shugaban hukumar kashe gobara ta kasa
  • Wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, ya nuna cewa Jaji zai karbi aiki ne daga hannun mukaddashin shugaban hukumar, Injiniya Karebo Samson
  • Kafin nadin nasa, ya kasance mataimakin kwanturola Janar mai kula da odar kayayyaki a hukumar kashe gobara ta tarayya

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Abdulganiyu Jaji a matsayin sabon shugaban hukumar kashe gobara ta kasa.

Labarin nadin nasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Misis Aisha Rufai, sakatariyar hukumar tsaron farin kaya, shige da fice da kuma gidajen yari (CDIPB) a ranar Talata, 26 ga watan Afrilu, a Abuja.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dan Najeriya ya fusata, ya maka Buhari a kotu saboda gallazawa 'yan Najeriya

Sanarwar ta kuma bayyana cewa nadin nasa ya fara aiki daga ranar 22 ga watan Afrilun 2022.

Da dumi-dumi: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci
Da dumi-dumi: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta rahoto cewa Jaji zai karbi aiki ne daga hannun mukaddashin shugaban hukuma, Injiniya Karebo Samson, wanda ya karbi rikon kwarya daga Alhaji Liman Ibrahim a watan Disamban 2021 bayan ya yi ritaya daga aiki.

Har zuwa lokacin da aka nada shi Injiniya Abdulganiyu shi ne mataimakin kwanturola Janar mai kula da odar kayayyaki a hukumar kashe gobara ta tarayya.

A cewar rahoton, sabon shugaban ya fara aiki a ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya a matsayin babban jami’in fasaha a 1991.

Ya riki mukamai daban-daban a ma’aikatar kafin aka mayar da shi ma’aikatar kashe gobara ta tarayya a 1999.

An haife shi a ranar 13 ga watan Agustan 1965 a cikin ahlin Alhaji Umar Olola Jaji a garin Ilorin, babbar birnin jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: kwamishinan gwamna Zulum ya yi murabus, zai tsaya takara kujerar yankinsu

Ya mallaki digiri na biyu a bangaren karatun injiniya a 1999 sannan yana da mata da yara.

Mawaki Rarara ya yiwa shugaban kasa Buhari wankin babban bargo a sabuwar wakarsa

A wani labari na daban, shahararren mawakin nan na siyasa wanda ya yi suna wajen wake shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu manyan yan siyasar arewa, Dauda Kahutu Rarara, ya magantu kan gazawar gwamnati mai ci a wata sabuwar waka.

A cikin wakar, Rarara ya jagoranci wata tawaga ta shahararrun mawakan Hausa karkashin 13X13, wata kungiya ta masana’antar Kannywood.

Lamarin ya haifar da zazzafan martani kan ko babban dan kashenin Buharin baya tare da shi kuma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel