Mawaki Rarara ya yiwa shugaban kasa Buhari wankin babban bargo a sabuwar wakarsa

Mawaki Rarara ya yiwa shugaban kasa Buhari wankin babban bargo a sabuwar wakarsa

  • Shugaban mawakar Muhammadu Buhari, Dauda Kahutu Rarara, ya caccaki gwamnatin shugaban kasar a cikin wata sabuwar wakarsa
  • Rarara ya yi magana a kan hauhawan rashin tsaro da ake fama da shi a birni da kauyukan kasar karkashin gwamnatin Buhari
  • Ya bayyana cewa a yanzu mutane kadan ne ke yiwa shugaban kasar uzuri domin gaba daya abubuwa sun tabarbare

Shahararren mawakin nan na siyasa wanda ya yi suna wajen wake shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu manyan yan siyasar arewa, Dauda Kahutu Rarara, ya magantu kan gazawar gwamnati mai ci a wata sabuwar waka.

A cikin wakar, Rarara ya jagoranci wata tawaga ta shahararrun mawakan Hausa karkashin 13X13, wata kungiya ta masana’antar Kannywood.

Lamarin ya haifar da zazzafan martani kan ko babban dan kashenin Buharin baya tare da shi kuma.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: kwamishinan gwamna Zulum ya yi murabus, zai tsaya takara kujerar yankinsu

Mawaki Rarara ya caccaki shugaban kasa Buhari a sabuwar wakarsa
Mawaki Rarara ya caccaki shugaban kasa Buhari a sabuwar wakarsa Hoto: Daily Trust
Asali: Instagram

Daily Trust ta rahoto cewa labarin sabuwar wakar ya shahara ne lokacin da kakakinsa, Rabi’u Garba Gaya, ya wallafa shi a shafinsa na Facebook.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A farkon shekarar da ta gabata ne mawakin ya jagoranci wani shiri inda ya bukaci yan Najeriya da su dauki nauyin wakarsa ta gaba da zai saki ta hanyar biyan N1000 kan kowani mutum daya.

Rarara ya ce yana so jama’a su dauki nauyin wata waka da zai jero nasarar gwamnatin Buhari.

Tun lokacin masoya suka zuba ido suna jiran ya saki wakar domin an rahoto cewa ya tara miliyoyin naira kan haka daga jama’a.

Sai dai kuma wasu sun yi Allah wadai da bukatar mawakin, inda suka bayyana shi a matsayin damfara yayin da wasu suka rantse cewa ba zai samu abun azo a gani don daukar nauyin wakar ba.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Ban yarda da tsarin karba-karba ba – Gwamna Bala Mohammed

Abun mamaki, masoyan mawakin sun cika da al’ajabi lokacin da ya yi waka kan rashin tsaro maimakon wakar yabon Buhari.

A cikin wakar, an soki Buhari kan gaza cika alkawarinsa na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Wani baiti a cikin wakar ya zo kamar haka:

“Yanzu fa jama’ar kasa kadan ke maku uzuri, don kuwa abun ya yawaita kauye da cikin gari. Ana jin wai-wai ada a yau gashi a zahiri. Fatana ni da kai mu daurata a mumbari.”

Wadanda suka fito a wakar sune Aminu Ladan Ala, Nura M Inuwa, Ali Isa Jita, da sauran manyan mawakan Hausa.

Shugaban kasa a 2023: Ban yarda da tsarin karba-karba ba – Gwamna Bala Mohammed

A wani labari, gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana cewa bai yarda da tsarin karba-karba ba gabannin zaben shugaban kasa na 2023 amma maimakon haka ya ce abun da ya kamata a mayar da hankali a kai shine neman shugaba da zai iya jagorantar Najeriya.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Kada Ka Ruɗa Ƴan Najeriya, Ƙungiya Ta Ja Kunnen Atiku

Gwamna Bala ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talbijin na Channels a shirin ‘Sunday Politics’.

Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan kungiyar dattawan arewa ta zabe shi da tsohon shugaban majalisar dattawa a matsayin yan takarar yarjejeniya na jam’iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel