Shirin 2023: kwamishinan gwamna Zulum ya yi murabus, zai tsaya takara

Shirin 2023: kwamishinan gwamna Zulum ya yi murabus, zai tsaya takara

  • Makusantan gwamna Zulum na Borno a siyasa suna ta aje mukamansu domin yin takara a zaben 2023
  • Ya zuw yanzu, an ce kusan mutum 10 ne suka ajiye aiki saboda su nemo kujerun siyasa a sansanin gwamnan
  • A wannan makon, kwamishinan yakar talauci na jihar ya yi murabus, ya bayyana aniyar shiga takara

Jihar Borno - Rahoton Punch ya ce, kwamishinan Yakar Talauci na Jihar Borno, Nuhu Clark, ya yi murabus daga mukaminsa domin tsayawa takarar dan majalisa a mazabar Chibok a karkashin jam’iyyar APC.

Clark ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a wata hira da ta yi da shi a Maiduguri ranar Litinin cewa ya yanke shawarar haka ne don gudanar da wakilci mai inganci ga mutanen Chibok.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Ban yarda da tsarin karba-karba ba – Gwamna Bala Mohammed

Kwamishina ya yi murasbu zai tsaya takarar majalisa
Shirin 2023: kwamishinan gwamna Zulum ya yi murabus, zai tsaya takara | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Clark, wanda aka zaba a matsayin shugaban karamar hukumar Chibok a 1999, ya ce har yanzu yana da alaka da jama’arsa kuma zai yi takara ne saboda su.

Ya yabawa Gwamna Babagana Zulum bisa yadda ya bashi damar zama kwamishina, ya kara da cewa gogewarsa a matsayinsa na tsohon shugaban kansila, shugaban matasan jihar, kuma mashawarci zai taimaka matuka a manufarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NAN ta kuma ruwaito cewa wani kwamishinan da ya yi murabus daga tawagar Zulum shi ne Bukar Talba daga ma’aikatar noma, kamar yadda Guardian ta tattaro.

Rahotanni sun bayyana cewa, Talba na neman tsayawa takara a kujerar majalisar tarayya ta a mazabar Nganzai/Monguno/Marte a karkashin jam’iyyar APC.

Akwai kuma wasu rahotanni da ba a tabbatar da ke cewa sama da mashawarta na musamman ga gwamnan 10 ne suka mika takardar murabus dinsu domin samun damar neman mukamai.

Kara karanta wannan

Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara

Zulum ya fara azuminsa a garin Mafa, ya raba N76m, kayan abinci ga talakawa sama da 15,000

A wani labarin na daban da muka kawo, Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya fara azuminsa na watar Ramadana a mahaifarsa, karamar hukumar Mafa dake tsakiyar jihar ta Borno.

Zulum a jawabin da ya saki ranar Asabar, 2 ga watan Afrilu, ya bayyana cewa da kansa ya jagoranci rabawa talakawa buhuhunan kayan abinci.

A cewar jawabin, akalla mutum 15,327 aka rabawa kudi a hannu da buhunanan shinkafa da sukari, da kuma atamfa na dinkin Sallah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel