Farashin kudin jirgin sama ya sake tashi gabannin bikin karamar sallah

Farashin kudin jirgin sama ya sake tashi gabannin bikin karamar sallah

  • Kamfanonin jiragen sama sun kara farashin kudadensu yayin da Al'ummar Musulmi ke shirye-shiryen bikin karamar sallah
  • Bincike ya nuna an fi samun tashin farashin ne a jiragen da za su tashi zuwa yankin arewa kamar su Abuja, Kano Katsina, Maiduguri, Yola da sauransu
  • Musulmai musamman mazauna yankunan kudancin kasar kan koma gida a yayin bukukuwan sallah domin yinsa cikin yan uwa da abokan arziki

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa yawancin kamfanonin jiragen sama sun kara farashin kudin jirginsu gabannin bukukuwan karamar sallah.

Saboda haka, yan Najeriya masu niyan tafiya gida sallah za su bude bakin aljihu ko kuma su bi hanya domin kamfanonin jirgin sun daga farashinsu.

Rahoton ya nuna cewa lamarin ya fi shafar yankunan arewacin kasar da suka hada da Abuja, Kano Katsina, Maiduguri, Yola da sauransu, inda ake sa Musulmai da dama za su tafi yin bikin Sallah.

Kara karanta wannan

Karin kudi 100%: Maniyyata aiki Hajji sun fusata, sun fito zanga-zanga, sun fadi bukatarsu

Farashin kudin jirgin sama ya sake tashi gabannin bikin karamar sallah
Farashin kudin jirgin sama ya sake tashi gabannin bikin karamar sallah Hoto: PM News
Asali: UGC

Yayin da farashin kudin jirgin zuwa wurare kamar Lagas-Abuja, Lagas-Port Harcourt da Lagas-Uyo da sauransu na nan a yadda suke kuma tsakanin N50,000, na zuwa arewa ya tashi inda wasu suka kai N122,000.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A watan Fabrairu wasu kamfanonin jirgi sun kara kudinsu zuwa akalla N50,000, lamarin da ya haddasa cece-kuce daga wasu yan Najeriya yayin da suma kamfanonin jirgin suka daura alhakin karin kan tsadar aiki.

Gwamnatin tarayya ta hukumomin FCCPC da NCAA sun shiga lamarin, inda suka bayyana abun a matsayin hadin baki, suka kuma nemi dole a janye shi.

Yayin da farashin bai chanja ba a wasu kamfanonin jirgi yan kadan, ana tsammanin fasinjojin da za su tafi gida sallah za su biya karin kudi domin ya yi tashin gwauron zabi gabannin bikin.

Bincike a shafukan kamfanonin jiragen ya nuna wasu sun nuna cewa akwai tashin farashi tsakanin 30% da 80% ga masu zuwa yawancin jihohin arewa.

Kara karanta wannan

An Shiga Ruɗani Da Firgici Yayin Da Ƙudan Zuma Suka Far Wa Mutanen Da Suka Tafi Ta'azziya Fadar Alaafin Na Oyo

Wannan karin ya shafi masu yankan tikiti daga ranar Laraba, 27 ga watan Afrilu har zywa 2 ga watan Mayu gabannin dogon hutun da ake shirin zuwa.

Yayin da Musulmai ke shirye-shiryen Sallah, ma’aikatan Najeriya na shirin tafiya hutun ranar ma’aikata ta 2022.

Amma wadanda ba su tsara tafiye-tafiyensu ta hanyar yankar tikiti da wuri ba, dole ne su siya tikitin jirgin da tsada.

Misali an saka tikitin Abuja zuwa Kano kan Max Air kan N100,000. Amma har zuwa yanzu yana kan N50,000 ne. tafiyar kimanin minti 40 ne.

Lagas zuwa Kano a Air Peace, wanda shima N50,000, a yanzu ya tafi kan N60,000 zuwa N70,000.

Hakazalika, Lagas zuwa Kano a jirgin Azman daga Alhamis, Juma’a, Asabar da Lahadi zai kama tsakanin N63, 878 da N94, 835.

Sai dai Abuja zuwa Maiduguri kan Azman Air na nan a kan N50,000 saboda gasar da ke kan hanyar.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugabanni a kudancin Kaduna sun koma ga Allah

Azman Abuja zuwa Gombe wanda tafiyar minti 45 yana kan farashin 63,878 yayin da Lagas zuwa Kano ke kan 63,878.

Mafi tsada a cikin dukka tikitin shine Lagas zuwa Sokoto, wanda ya kai tsakanin 108,214 zuwa 122,196 a Arik Air. Jirgin na zuwa Sokoto sau uku a sati.

Mawaki Rarara ya yiwa shugaban kasa Buhari wankin babban bargo a sabuwar wakarsa

A wani labari na daban, shahararren mawakin nan na siyasa wanda ya yi suna wajen wake shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu manyan yan siyasar arewa, Dauda Kahutu Rarara, ya magantu kan gazawar gwamnati mai ci a wata sabuwar waka.

A cikin wakar, Rarara ya jagoranci wata tawaga ta shahararrun mawakan Hausa karkashin 13X13, wata kungiya ta masana’antar Kannywood.

Lamarin ya haifar da zazzafan martani kan ko babban dan kashenin Buharin baya tare da shi kuma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel