An Shiga Ruɗani Da Firgici Yayin Da Ƙudan Zuma Suka Far Wa Mutanen Da Suka Tafi Ta'azziya Fadar Alaafin Na Oyo

An Shiga Ruɗani Da Firgici Yayin Da Ƙudan Zuma Suka Far Wa Mutanen Da Suka Tafi Ta'azziya Fadar Alaafin Na Oyo

  • Gungun kudan zuma sun harbi wasu mutane cikin wadanda suka tafi fadar Alaafin na Oyo domin yin ta'aziyyar rasuwar sarkin
  • Daga bisani mutanen sun rika karyo reshen bishiyoyi da ganyaye suka rika korar kudan zuman cikin wadanda zuman suka harba harda dan sanda
  • Marigayi Oba Lamidi Adedeyi ya rasu ne a daren ranar Juma'a kuma ana sa ran yi masa jana'iza a yau bayan Asabar

Jihar Oyo - Kudan zuma sun kai wa wasu daga cikin mutane da suka tafi fadar Alafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi hari a ranar Asabar yayin da suka tafi yin ta'aziyya.

The Punch ta rahoto cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 10 na safe bayan malaman addinin musulunci domin shirin jana'izar Oba Adeyemi, wanda ya mutu a daren ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Maziyarta da maniyyata 51 sun yi hadarin mota a Madina, mutum 8 sun kwanta dama

Kudan Zuma Sun Kai Wa Mutane Hari a Wurin Ta'aziyyar Alaffin Na Oyo
Kudan Zuma Sun Kai Wa Mutane Hari a Wurin Ta'aziyyar Alaffin Na Oyo. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Rahoton ya nuna cewa an hangi wasu daga cikin mutanen da kudar zuman suka kai wa harin sun karyo reshe da ganye daga bishiya domin korar su.

Wani jami'in dan sanda na cikin wadanda kudan zuman suka kai wa hari kuma wasu daga cikin mutanen da ke wurin sun taimaka masa wurin korar zuman da suka manne a kayansa.

Basorun na Oyo ta karbi mulkin fadar Alaafin kafin a nada sabon Alaafin

A bangare guda, Jagoran Oyomesi, Basorun na Oyo, High Chief Yusuf Akinade, zai rika kula da jagorancin fadar Alaafin na Oyo, har zuwa lokacin da za a nada sabon Alaafin.

Hakan na zuwa ne bayan rasuwar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, a daren ranar Juma'a.

A tarihi, Basorun ne ke da wuka da nama wurin nada sabon Alaafin. A cewar tarihin, Masarautar Oyo tana karkashin jagorancin Alaafin ne, a matsayin sarki.

Kara karanta wannan

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Marigayi Sarkin Oyo, Alaafin Lamidi Adeyemi

Tunda farko, kun ji cewa da safiyar Asabar aka samu labarin cewa Allah ya yiwa Sarkin Oyo, babbar Sarki a kasar Yarbawa, Oba Lamidi Adeyemi, rasuwa.

Oba Adeyemi ya mutu ne da yammacin Juma'a a Asibitin koyarwa jami'ar Afe Babalola dake Ado Ekiti, rahoton Premium Times.

Cikin dare aka gaggauta kai gawarsa jihar Oyo domin fara shirin jana'izarsa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel