Rashin tsaro: Shugabanni a kudancin Kaduna sun koma ga Allah

Rashin tsaro: Shugabanni a kudancin Kaduna sun koma ga Allah

  • Shugabannin al'umman Kirista a yankin kudancin Kaduna sun yanke shawarar komawa ga Allah domin samun saukin matsalar tsaro da ya addabe su
  • Tuni dai kungiyar kiristocin yankin suka kafa wani kwamitin mutum hudu domin jagorantar gangamin taron addu'o'i
  • A baya su kan yi irin wannan taro duk shekara amma tsawon shekaru biyu kenan ba a yi ba sakamakon annobar korona

Kaduna - Duba ga hauhawan matsalar rashin tsaro a yankin, kungiyar shugabannin kirista a kudancin Kaduna sun kafa wani kwamitin mutum hudu don taron addu’a na wannan shekarar.

Tsawon shekaru biyu kenan ba a gudanar da taron addu’an ba wanda aka saba yi duk shekara saboda annobar korona, jaridar Punch ta rahoto.

Rashin tsaro: Shugabanni a kudancin Kaduna sun koma ga Allah
Rashin tsaro: Shugabanni a kudancin Kaduna sun koma ga Allah Hoto: Punch
Asali: UGC

Da yake rantsar da kwamitin a ranar Laraba a garin Kafanchan, jim kadan bayan taron mika masa shugabanci, shugaban kungiyar, Dr. Emmanuel Kure, ya bukaci mambobin kwamitin da su jajirce wajen ganin an cimma nasara a taron.

Kara karanta wannan

Kwakwaf: Hotunan da ba kasafai ake gani ba sun nuna abincin da Buhari ke ci a lokacin buda baki

Ya bayyana taron addu’an a matsayin mai muhimmanci, cewa za a yi addu’o’i domin dawo da yancin kasar.

Kure ya yi godiya ga tsohon shugabancin kungiyar kan sadaukarwar da suka yi a zamaninsu sannan ya nemi goyon bayan mambobin sabon shugabancin domin yin nasara.

Ya yi kira ga mambobinsu, musamman shugabanni, da su tsarkake kansu don ci gaban kasa da mutanensu Within Nigeria ta rahoto.

Yan bindiga sun yi barazanar aurar da wata budurwa da suka sace a Neja idan ba a biya kudin fansa N1.7m ba

A wani labari na daban, yan bindiga sun yi barazanar aurar da wata budurwa mai shekaru 21 da suka sace daga wani gari a jihar Neja idan har iyayenta basu biya kudin fansarta naira miliyan 1.7 ba, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi buda baki da gwamnoni, shugabannin tsaro da sauransu

A ranar Asabar da ya gabata ne dai aka yi garkuwa da wasu mutane a hanyar Tapila-Gwada a karamar hukumar Shiroro ta jihar, kuma budurwar na daya daga cikinsu.

A yayin farmakin da suka kai garin, wanda yake tafiyar minti 30 daga garin Minna, babban birnin jihar, wasu mazauna garin Tapila sun yi nasarar tserewa jim kadan bayan yan bindigar sun sace su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel