Karin kudi 100%: Maniyyata aikin Hajji sun fusata, sun fito zanga-zangar huce haushi

Karin kudi 100%: Maniyyata aikin Hajji sun fusata, sun fito zanga-zangar huce haushi

  • Maniyyata aikin Hajjin bana sun fusata da karin kudin jigilar kai su kasa mai tsari don gudanar da ibada
  • Sun koka da karin fiye da kashe 100, wanda ya jawo tsaiko ga wasu ta hanyar nemo kudin cikon cikin kankanin lokaci
  • Wasu a jihar legas, sun fito zanga-zanga, sun bayyana abubuwan da suke so gwamnati ta tsoma baki akai

Jihar Legas - Wasu maniyyata aikin Hajjin bana a jihar Legas a ranar Litinin sun mamaye gidan gwamnatin Alausa domin nuna rashin amincewarsu da karin 100% na farashin kudin kujerar Hajjin 2022.

Daily Trust ta ruwaito cewa, alhazan sun ce tuni sun biya kudin aikin Hajjin 2020 tun shekarar 2019 da ba a yi Hajji ba saboda annobar Korona.

Kara karanta wannan

Miyetti Allah: Ƴan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mambobinmu 10 Da Shanu 300, Sun Buƙaci N4m Da Bindiga Ɗaya a Anambra

Sun ce abin ya ba su mamaki, sun samu sako ne kwatsam daga Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar cewa su biya karin N1.3m domin cike kudaden da suka biya tun 2019.

Zanga-zangar mahajjata
Karin kudi 100%: Maniyyata aiki Hajji sun fusata, sun fito zanga-zangar huce haushi | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC
Daya daga cikin masu zanga-zangar da ya ce su wakilan maniyyata Hajjin bana ne daga dukkan kananan hukumomin jihar, ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mun zo nan ne don kokawa kan batun kudin. Makwanni uku da suka wuce, Kwamishina ya gayyace mu zuwa tsohon ginin sakatariya. Sai aka ce mana za su kara kudin ne amma kadan, sai muka roki kada a kara da yawa.
“Mun biya N1.3m a 2019, abin mamaki, a ranar Juma’a, mun samu sakon karin 1,340,000, wanda ya kai 2,640,000 kenan, fiye da 100%. Kuma yanzu suna ba mu wa'adin kwanaki biyar na aiki ga maniyyatan 2019, 2020, 2021 da 2022."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDLEA ta kai samame wurin bikin casu a Abuja, ta cafke jama'a da yawa

Sun bukaci gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu da kakakin majalisar dokokin jihar, Mudashiru Obasa su sa baki a lamarin.

Aikin Hajji zai tashi a shekarar bana, kudin sauke farali zai karu da fiye da 50% inji NAHCON

A wani labarin, hukumar nan ta National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON) mai kula da aikin Hajji a Najeriya ta ce kudin aikin wannan shekarar zai karu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban hukumar NAHCON na kasa, Zikrullah Hassan yana cewa hasashensu ya nuna kudin kujera zai karu da akalla 50%.

Abin da mahajatta suka biya a shekarar 2019 ya kai N1.5m. maganar da ake yi a bana, duk wadanda suka bada kudi tun 2020 sai sun cika akalla N1m.

Asali: Legit.ng

Online view pixel