Shirin 2023: Kwankwaso ya lale N30m, ya sayi fom din takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP

Shirin 2023: Kwankwaso ya lale N30m, ya sayi fom din takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP

  • Fitaccen dan siyasar Arewa, kuma jigon tafiyar kwankwasiyya ya sayi fom din takarar shugaban kasa
  • Ya bayyana sha'awarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 a karkashin jam'iyyar NNPP mai tasowa
  • Kwankwaso dai bai jima da shigowa jam'iyyar NNPP ba, lamarin da ya sauya akalar siyasar Kano da wasu sassan Arewa

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya zare makudan kudade har Naira miliyan 30 ya sayi fom din tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Jagoran kungiyar Kwankwasiyya Kwankwaso ya samu tarba mai kyau daga shugaban jam’iyyar na kasa, Farfesa Rufa’i Alkali da sakataren kwamitin tsare-tsare na jam'iyyar na kasa, Sanata Suleiman Hunkuyi da sauran mambobin kwamitin ayyuka na NNPP.

Kwankwaso ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa a 2023
Shirin 2023: Kwankwaso ya lale N30m, ya sayi fom din takara a jam'iyyar NNPP | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kwankwaso, wanda tsohon ministan tsaron ne ya yi watsi da jam’iyyar APC mai mulki da kuma PDP, inda ya kira su jam'iyyun siyasa da aka baiwa damar gudanar da mulkar ‘yan Najeriya amma suka gaza.

Kara karanta wannan

Ngige ya ayyana shiga takarar shugaban kasa a 2023, ya faɗi wasu kalamai kan Buhari da APC

Jaridar Aminiya ta yada wasu hotuna na Sanata Rabiu Musa Kwankwaso lokacin da yake karbar fom din takarar dags shugabannin jam'iyyar ta NNPP a babban birnin tarayya Abuja.

Tun farko, masoya Kwankwaso sun shaida wa wakilinmu cewa, suna tare da Kwankwaso a duk jam'iyyar da ya tsinci kansa, saboda shi suke goyon baya ba jam'iyya ba.

Zaben 2023: Kwankwaso na shirin bayyana aniyarsa ta danewa kujerar Buhari

A wani labarin, bayan cece-kuce da shirye-shiryen siyasa, a yammacin yau (Talata) tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso zai bayyana sha'awar tsayawa takarar shugabancin kasa a jam'iyyar New Nigeria Peoples Party.

Jaridar Punch ta samu labari daga wani jigon jam’iyyar cewa jigon ‘yan siyasar daga yankin Arewa maso Yamma, mutumin Kano da sauran mabiyansa sun isa Abuja domin halartar taron.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kwankwaso na shirin bayyana aniyarsa ta danewa kujerar Buhari

A cewar wani dan jam'iyyar: "Mai martaba (Kwankwaso) yanzu ya kira ni, cewa zai bayyana aniyar takarar shugaban kasa a yau a Abuja."

An ruwaito cewa Kwankwaso, wanda kuma tsohon ministan tsaro ne, a watan Fabrairu ya sanar da kafa wata tafiyar siyasa mai suna National Movement (NM), domin sauya akalar yadda ake tafiyar da siyasa a Najeriya a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel