Yafewa Dariye da Nyame: Fadar shugaba Buhari ta mayarwa Wike da zazzafan martani, ta ce yana ihu ne bayan hari

Yafewa Dariye da Nyame: Fadar shugaba Buhari ta mayarwa Wike da zazzafan martani, ta ce yana ihu ne bayan hari

  • A makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa Gwamna Jolly Nyame da takwaransa Joshua Dariye afuwa
  • Sai dai hakan bai yiwa Gwamna Nyesom Wike dadi ba, harma ya dasa ayar tambaya a kan wannan mataki na shugaban kasar
  • A martaninta, fadar shugaban kasa ta ce gwamnan na ihu ne bayan hari domin kamata ya yi ya bayyana ra’ayinsa tun a wajen taron yafiyar domin an gayyace shi

Abuja - Fadar shugaban kasa ta mayarwa gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, martani kan sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi saboda yafe wa tsohon gwamnan jihar Filato, Joshuwa Dariye da takwaransa na Taraba, Jolly Nyame wadanda aka daure akan rashawa.

Kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya bayyana cewa sukar da gwamnan ya yi bata da wata fa’ida.

Kara karanta wannan

A Yayin Da Ortom Ya Yabi Buhari, Wike Ya Masa Kaca-Kaca Kan Yi Wa Dariye Da Nyame Afuwa

Wike dai ya ce afuwar alama ce da ke nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta raina wa ‘yan Najeriya hankali kuma siyasa kawai take yi ba yaki da rashawa ba.

Yafewa Dariye da Nyame: Fadar shugaba Buhari ta mayarwa Wike da zazzafan martani, ta ce yana ihu ne bayan hari
Yafewa Dariye da Nyame: Fadar shugaba Buhari ta mayarwa Wike da zazzafan martani, ta ce yana ihu ne bayan hari Hoto: Buhari Sallau, Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON
Asali: Facebook

Wike ya yi wannan maganar ne yayin da ya kai ziyara garin Minna, babbar birnin jihar Neja don kamfen ga wakilan jam’iyyar PDP.

Ya ce:

“In fada muku gaskiya, wannan gwamnatin ta APC ta yaudarmu kwarai. Gwamnatin ta ce tana yaki da rashawa amma zaben mutane take yi ta dauresu bayan sun gama shari’a a kotun koli.
“Daga bisani kuma sai su saki mutanen da ke gidan yari wadanda suka ce duk ‘yan rashawa ne. Wacce irin gwamnati ko kuma kasa ce wannan?
“Sun yi hakan ne don siyasa, zabe ya kusa zuwa kuma suna son Dariye ya taimaki jam’iyyarsu a Jihar Filato. Sannan suna bukatar taimakon Nyame a Jihar Taraba. Me ya hana su yafe wa James Ibori, misali.”

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Ya Bayyana Lokacin Da Zai Ƙaddamar Da Takararsa Na Shugabancin Ƙasa

Da yake martani a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook, Shehu ya ga laifin sukar da Wike ya yi, yana mai cewa kamata ya yi ace gwamnan ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsakin da aka yi afuwar, wanda ya halarta maimakon watsa ra’ayinsa bayan taron.

Shehu ya ce:

“Ban ga fa’idar sukar hukuncin gwamnati na yafewa gwamna Dariye da takwaransa Nyame da Wike ya yi ba alhalin an gayyace shi wajen taron amma ya ki halarta.
“Mataimakiyar gwamnan jihar Ribas, Dr. Ipalibo Banigo, wacce ta halarci taron masu ruwa da tsakin ta yanar gizo ta toshe kamararta ta yadda zai yi wuya mutum ya yanke ko ta zauna a bayan kwanfutar mai duhu ko kuma kawai ta yi tafiyarta ne bayan ta shiga taron da farko.
“Idan batun yafiyar bai yiwa gwamnan dadi ba, abun da ya kamata shine shi ko wakiliyarsa su zauna har a gama taron sannan su bayyana ra’ayinsu. Bai aikata haka ba. Sakin jawabi a kafar watsa labarai bayan taron siyasa ce kawai.”

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso na hararo kujerar Buhari, ya ce tazarcensa ba ta amfani Najeriya da komai ba

Buhari ya yafewa Joshua Dariye, Jolly Nyame, da wasu fursunoni 157

A baya mun kawo cewa Majalisar kolin kasa (masu mulki da tsaffin shugabanni) ta yafewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame da tsohon gwamnan Plateau, Joshua Dariye, dake garkame a kurkuku yanzu.

Gwamnonin biyu na cikin fursunoni 159 da majalisar ta yafewa ranar Alhamis karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, rahoton Premium Times.

Daga cikin wadanda aka yafewa tsohon soja da minista lokacin Abacha, Tajudeen Olanrewaju; Laftanan Kanar Akiyode, da dukkan Sojojin da aka daure kan laifi a hannu cikin yunkurin juyin mulkin Gideon Orkar a 1990.

Asali: Legit.ng

Online view pixel