Harin jirgin Abj-Kad: FG ta ki yarda da bukatar sakin kwamandojin 'yan bindiga kafin sako wadanda aka sace
- Tattaunawar da gwamnati ke yi da yan ta'adda domin karbo mutanen da aka sace a harin jirgin kasan Kaduna ya hadu da cikas
- Hakan ya kasance ne saboda gwamnatin tarayya ta ki yarda da bukatun yan bindigar na sakin wasu kwamandojinsu 16
- Hakazalika gwamnati ta ce ba za ta biya kudin fansa kan mutanen ba domin ta yi hakan a baya amma babu wani tasiri da ya yi
Akwai alamu da ke nuna an samu tsaiko a tattaunawar da ke gudana tsakanin gwamnatin tarayya da yan ta’addan da suka farmaki jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja a ranar 28 ga watan Maris, bayan gwamnati ta ki yarda da bukatun su.
Yan ta’addan na rike da kimanin fasinjoji 100 da suka sace a lokacin harin jirgin kasan, wanda ya afku a Katari, Kaduna, bayan sun dana nasa bam.
An kashe mutane takwas sannan wasu 26 sun jikkata a yayin da yan bindigar suka budewa jirgin wuta sannan a lokacin ne suka sace mutanen da ke hannunsu a yanzu.
Hukumar kula da jirgin kasan Najeriya ta ce bata samu ji daga fasinjoji 163 da ma’aikatan jirgin bakwai, wadanda ke cikin jirgin kasan a lokacin da aka kai farmakin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An tattaro cewa maharan sun bukaci a saki kwamandojinsu da masu daukar nauyinsu guda 16 da ke tsare a madadin mutanen da suka sace amma gwamnati bata yarda da hakan ba.
Majiyoyin tsaro sun ce hukumomi na kan tattaunawa da yan ta’addan, yayin da suke amfani da wasu hanyoyi domin ceto wadanda aka sace.
Jaridar Punch ta kuma tattaro cewa gwamnati bata da niyan biyan kudin fansa a kan wadanda aka sacen.
Wata majiya ta ce:
“Gwamnatin tarayya na duba bukatunsu saboda wadanda suka sace, amma gwamnati na taka-tsan-tsan; ba za ta iya cika bukatun yan ta’addan ba. A baya da gwamnati ta saki wasu kwamanjoji, sun koma sannan ta’addanci ya sake ta’azzara.
“Don haka babu wanda ke duba yiwuwar sakin kwamandojin. An kuma ba yan ta’addan kudi a baya kuma lamarin bai inganta ba.
Sakamakon rashin ci gaba a tattaunawar, an tattaro cewa mai yiwuwa yan bindigar su fara neman kudin fansa daga yan uwan wadanda suka sace.
Wasu iyalan sun yi zanga-zanga kan sace yan uwansu sannan sun yi korafin cewa yan ta’addan basu tuntube su ba tun bayan da suka sace su kimanin makonni biyu da suka gabata.
A halin da ake ciki, Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya ba da umarnin zuba tsauraran matakan tsaro a duk wuraren jama’a da kuma muhimman wuraren gwamnati gabanin bikin Easter.
An kaiwa jirgin kasan Abuja-Kaduna hari ne don koyawa El-Rufa'i darasi
A wani labari, yan bindigan da suka kai harin jirgin kasar Abuja-Kaduna makonnin da suka gabata sunce sun kari jihar Kaduna ne don koyawa Gwamna Nasir El-Rufa'i darasi.
Wani Mutumin mai suna Dr AbdulKarim Attah, wandan dan uwan wata mata yar shekara 85 cikin wadanda aka sace yace haka yan bindigan suka bayyana masa, TheNation ta ruwaito.
Attah, ya ruwaito yan bindigan da cewa "gwamnan jihar ya dade yana wage bakinsa yadda yaga dama kuma hakan yasa suka kai hari gidansa."
Asali: Legit.ng