Harin jirgin Abj-Kad: Gwamnatin Buhari ta fara tattaunawa da 'yan bindiga

Harin jirgin Abj-Kad: Gwamnatin Buhari ta fara tattaunawa da 'yan bindiga

  • Rahotanni daga jihar Kaduna sun bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da 'yan bindiga
  • Wannan tattaunawa na zuwa ne daidai lokacin da wa'adin da 'yan uwan wadanda aka sace suka ba gwamnati ya kare
  • An sace jama'a a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, lamarin da ya tada hankalin 'yan Najeriya da dama

Jihar Kaduna - Gwamnatin tarayya ta bude kafar tattaunawa da ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjoji sama da 60 a cikin wani jirgin kasa mai zuwa Kaduna makwanni biyu da suka gabata, kamar yadda ‘yan uwan ​​wadanda abin ya shafa suka bayyana.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, akalla mutane tara ne aka kashe tare da yin garkuwa da sama da 60 a lokacin da ‘yan ta’adda suka dasa bama-bamai a kan hanyar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, lamarin da ya tilasta wa jirgin da aka kai wa hari ya kauce hanya.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

Harin 'yan bindiga a Kaduna: An fara tattaunawa da 'yan bindiga
Gwamnatin Buhari ta fara tattauna da wadanda suka sace fasinjojin jirgin Abj-Kad | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Daga nan ne ‘yan ta’addan suka bude wuta kan jirgin kana suka yi awon gaba da gomman mutane a yammacin ranar 28 ga Maris, 2022.

Sai dai bayan kwanaki tara da kai harin, ‘yan ta’addan sun sako manajan Daraktan Bankin noma, Alwan Hassan, bayan biyan Naira miliyan 100 na fansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da suke zantawa da manema labarai a Kaduna, ‘yan uwa da abokan arzikin fasinjojin da aka sace a ranar Juma’a, sun ce gwamnatin tarayya ta ba su tabbacin cewa an bude hanyar tattaunawa da ‘yan ta’addan.

A cewar wani Dokta Jimoh Fatai, wanda aka nada a matsayin shugaban kungiyar da ke neman a sako ‘yan uwan wadanda aka sace:

“Bayan zaman majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a ranar Laraba, mun ji ta bakin gwamnatin tarayya ta bakin ministan yada labarai, Lai Mohammed cewa gwamnati na cikin tattaunawa. Cewa tuni dai gwamnatin ta fara tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da ‘yan uwanmu.

Kara karanta wannan

Ashe makiyaya ne ba ‘Yan bindiga ba – ‘Yan Sanda sun yi karin haske kan bidiyon da ke yawo

“Mun yi farin ciki da hakan, mun lura da hakan, mun amince kuma mun yaba da kokarin gwamnati kan hakan. Abin da muke nema a yanzu shi ne gwamnati ta gaggauta aiwatar da aikin.”

An ruwaito wannan labarin ya zo ne a daidai lokacin da wa'adin sa'o'i 72 da 'yan dangin suka bayar ga gwamnatin Najeriya domin a bude tattaunawar da za ta sa a sako mutanen, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Dokta Fatai ya ce tun da aka fara tuntubar ‘yan ta’addan har yanzu ba su tuntube su ba kan halin da ‘yan uwansu ke ciki duk da cewa sun nuna damuwa cewa wadanda aka kama za su shiga mawuyacin hali a lokacin damina.

Kungiyar ta gargadi hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya kan duk wani yunkuri na dawo da zirga-zirgar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna inda ta jaddada cewa ya kamata a ba da fifiko kan tsaro da kuma sako wadanda ke hannun 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Abuja ba ta zaman irinku bane: 'Yan sanda sun kama masu sana'ar 'Bola Jari'

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

A wani labarin, akalla mutane 106 ne ya zuwa yanzu aka ce an binne sakamakon hare-haren da aka kai kan al’umomin jihar Filato a kwanakin nan.

Shugaban karamar hukumar Kanam ta jihar Filato Dayabu Garga ne ya bayyana hakan, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Da yake karin haske game da sake barkewar rikici a wasu sassan jihar ta Arewa ta Tsakiya, Garga ya ce: "Ina nan a ranar Litinin da safe lokacin muka yi jana'izar mutane 106 da aka kashe kuma muna ci gaba da diban gawarwaki a nomaki."

Asali: Legit.ng

Online view pixel