An kaiwa jirgin kasan Abuja-Kaduna hari ne don koyawa El-Rufa'i darasi

An kaiwa jirgin kasan Abuja-Kaduna hari ne don koyawa El-Rufa'i darasi

  • Iyalan wasu daga cikin wadanda aka sace a jirgin Abuja-Kaduna sun bayyana abinda yan bindigan suka fada musu
  • Wani mutumi wanda aka sace yar uwarsa yace yan bindigan sun ce maganganun El-Rufa'i ya sa suka kai hari
  • A cewarsa, yan bindigan da sun ce yanzu suka fara addabar jihar Kaduna

Kaduna - Yan bindigan da suka kai harin jirgin kasar Abuja-Kaduna makonnin da suka gabata sunce sun kari jihar Kaduna ne don koyawa Gwamna Nasir El-Rufa'i darasi.

Wani Mutumin mai suna Dr AbdulKarim Attah, wandan dan uwan wata mata yar shekara 85 cikin wadanda aka sace yace haka yan bindigan suka bayyana masa, TheNation ta ruwaito.

Attah, ya ruwaito yan bindigan da cewa "gwamnan jihar ya dade yana wage bakinsa yadda yaga dama kuma hakan yasa suka kai hari gidansa."

Kara karanta wannan

Harin jirgin Abj-Kad: Gwamnatin Buhari ta fara tattaunawa da 'yan bindiga

Ya ce yan bindigan sun ce yanzu suka fara.

Dr Attah yace sau 11 yana magana a wayar tarho da yan bindigan kuma dalilin da suka bada kenan.

Jirgin kasan Abuja-Kaduna
An kaiwa jirgin kasan Abuja-Kaduna hari ne don koyawa El-Rufa'i darasi Hoto: NRC
Asali: UGC

Harin jirgin Abj-Kad: Gwamnatin Buhari ta fara tattaunawa da 'yan bindiga

Gwamnatin tarayya ta bude kafar tattaunawa da ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjoji sama da 60 a cikin wani jirgin kasa mai zuwa Kaduna makwanni biyu da suka gabata, kamar yadda ‘yan uwan ​​wadanda abin ya shafa suka bayyana.

Da suke zantawa da manema labarai a Kaduna, ‘yan uwa da abokan arzikin fasinjojin da aka sace a ranar Juma’a, sun ce gwamnatin tarayya ta ba su tabbacin cewa an bude hanyar tattaunawa da ‘yan ta’addan.

A cewar wani Dokta Jimoh Fatai, wanda aka nada a matsayin shugaban kungiyar da ke neman a sako ‘yan uwan wadanda aka sace:

Kara karanta wannan

Yan bindiga da yan Boko Haram sun fara alaka da juna, Gwamnatin tarayya ta sanar

“Bayan zaman majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a ranar Laraba, mun ji ta bakin gwamnatin tarayya ta bakin ministan yada labarai, Lai Mohammed cewa gwamnati na cikin tattaunawa. Cewa tuni dai gwamnatin ta fara tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da ‘yan uwanmu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel