Yan bindiga da yan Boko Haram sun fara alaka da juna, Gwamnatin tarayya ta sanar

Yan bindiga da yan Boko Haram sun fara alaka da juna, Gwamnatin tarayya ta sanar

  • Daga karshe, gwamnatin tarayya ta tabbatar da labarin cewa yan Boko Haram suka kai hari jirgin kasan Abuja-Kaduna
  • Lai Mohammed yace ba zai fadawa yan jarida matakan da suke dauka wajen fansar wadanda aka sace ba
  • Mun kawo muku cewa yan bindigan suna bukatar a saki kwamandojinsu 16 dake tsare hannun gwamnati don su saki wadanda suka sace a harin ranar 28 ga Maris.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa binciken farko-farko da ta gudanar kan harin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya nuna cewa an fara samun hadin kai tsakanin yan bindiga da yan Boko Haram.

Daily Trust ta rahoto cewa Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan zaman majalisar zartaswar da shugaba Buhari ya jagoranta ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda hudu har lahira

Yan Ansaru
Yan bindiga da yan Boko Haram sun fara alaka da juna, Gwamnatin tarayya ta sanar Hoto: DailyNigerian
Asali: Facebook

Lai Mohammed, wanda yayi jawabi bayan jawabin Minista tsaro, Bashir Salihi Magashi, ya yi tsokaci kan halin da ake ciki kan wadanda aka sace a jirgin kasan.

Yace:

"Abinda ke faruwa shine akwai wani sabon alaka tsakanin yan bindiga da yan ta'addan Boko Haram."
"Binciken farko-farko sun nuna cewa abinda ya faru a harin jirgin kasan Abuja ya nuna akwai alaka tsakanin yan bindiga da yan Boko Haram daga Arewa maso gabas. Ina tabbatar muku da cewa gwamnati na iyakan kokarinta."

Yayinda aka tambayesa shin me gwamnati ke yi kan wa'adin kwanaki uku da yan bindiga suka bada kan wadanda suka sace, yace:

"Game da matakan da muke dauka kan wannan lamari, ba zamu fallasawa yan jarida ba, saboda kada muyi wasa da rayukan mutanen (dake hannun yan bindigan."

Kara karanta wannan

Jami’an tsaro sun yi nasarar dakile wani hari kan kauyen Kaduna, sun kashe dan bindiga 1

Ku saki kwamandoji da masu daukar nauyinmu 16 matsayin fansar wadanda muka sace, Yan bindiga

Yan bindigan da suka kai hari jirgin kasan Abuja, suna bukatar a saki kwamandojinsu 16 dake tsare hannun gwamnati don su saki wadanda suka sace a harin ranar 28 ga Maris.

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa yan bindiga sun kai harin ne saboda mika wannan bukata.

A ranar Litinin, Punch ta ruwaito cewa yanzu haka ana tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da yan bindigan.

Wani babban jami'in gwamnati da aka sakaye sunansa yace yan bindigan sun wahala bisa kama kwamandoji da masu daukar nauyinsu.

Mutum daya kadai suka saki, amma sun saki bidiyo 2

A makon da ya gabata, yan bindigan sun saki Diraktan bankin noma, Alwan Hassan.

A bidiyon farko da suka saki ranar Laraba 6 ga Afrilu, sun bayyana cewa ba kudi suke bukata ba, gwamnati ta san abinda suke bukata.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kutsa cikin Masallaci, Sun bindige Sarki har Lahira ana Sallar Isha'i

Sun haska bidiyon ne tare da Shugaban bankin noma, Alwan Hassan, inda suka ce zasu sake shi albarkacin tsufarsa da watar Ramadan.

A ranar Lahadi kuma suka sake sakin wata bidiyon inda wasu daga cikin wadanda suka sace suka yi magana.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel