2023: ‘Dan takarar APC ya musanya rade-radin hakura da neman zama Shugaban kasa

2023: ‘Dan takarar APC ya musanya rade-radin hakura da neman zama Shugaban kasa

  • Francis Nwaze ya ce babu gaskiya a rahotannin da ke yawo a kan janye takarar David Umahi a APC
  • Hadimin na Gwamnan jihar Ebonyi ya ce Mai girma Umahi zai nemi takarar shugaban kasa a 2023
  • Hakan ya saba jita-jitar da ake ji cewa Gwamnan ya hakura, zai yi takarar Sanatan Ebonyi ta Kudu

Ebonyi - Francis Nwaze wanda ya na cikin masu magana da yawun Dave Umahi, ya yi watsi da jita-jitar cewa gwamnan Ebonyi ya hakura da shiga takara.

Premium Times ta rahoto Mista Francis Nwaze yana cewa Gwamna Dave Umahi yana nan a kan bakarsa na neman kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

A makon nan rahotanni suka fara yawo cewa Mai girma Dave Umahi ya koma neman tikitin Sanatan kudancin jihar Ebonyi a maimakon na shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin sunayen masu takarar shugaban kasa na APC da PDP

Da aka tuntubi Nwaze domin jin gaskiyar abin, ya tabbatarwa manema labarai cewa uban gidan na sa bai taba janyewa daga neman tutar shugaban kasa ba.

Mai magana da yawun Gwamnan ya shaidawa jaridar cewa labaran karya ne kurum wasu makiyan Umahi suke yadawa domin kawowa siyasarsa cikas.

A cewar Mista Francis Nwaze, wasu abokan hamayya ne suka biya ake yada irin wannan labari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Dan takarar Shugaban kasa
Gwamna Dave Umahi Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC
“Har yanzu Gwamna Umahi ya na cikin masu neman tikitin shugaban kasa. Rahoton ba komai ba ne face furofaganda.” - Mr. Francis Nwaze.

Umahi zai samu takara a APC

Bugu da kari, da yake maida martani a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu 2022, Nwaze ya ce yana sa ran Umahi zai yi nasarar zama ‘dan takarar APC a zaben 2023.

Hadimin ya na ganin Gwamnan zai doke kowa domin ya rikewa jam’iyya tutar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Osinbajo: Idan Tinubu ya kawo ka siyasa, ka janye niyyar takarar Shugaban kasa – Jigon APC

Kafin Umahi ya iya zama wanda zai yi wa APC takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, dole ya doke Bola Tinubu, Yemi Osinbajo, da irin su Rotimi Amaechi.

Gwamnonin Najeriya su kan nemi kujerar majalisar dattawa da zarar sun ga wa’adinsu ya zo karshe. Zuwa yanzu Umahi ba zama Sanata ne a gabansa ba.

Ba zan nemi Sanata ba - Wike

A gefe guda a PDP, an ji labarin Gwamnan Ribas watau Nyesome Wike ya ziyarci jihar Kuros Riba a kokarin da yake yi na ganin ya samu takarar shugaban kasa.

Wike ya ce ba zai goyi bayan a zauna domin a fito da ‘dan takara ba tare da yin zabe ba. Sannan ya ce bai da niyyar janye takara ko ya koma harin kujerar Sanata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel