Jerin ‘yan siyasa 35 da suka fito takara zuwa yanzu, su na hangen kujerar Buhari a Aso Villa

Jerin ‘yan siyasa 35 da suka fito takara zuwa yanzu, su na hangen kujerar Buhari a Aso Villa

  • ‘Yan siyasa kusan 40 sun shaidawa Duniya cewa za su nemi kujerar shugaban Najeriya a zaben 2023
  • Farfesa Yemi Osinbajo shi ne wanda ya ayyana burinsa a karshe, zai nemi tikiti ne a jam’iyyar APC
  • Masu neman takarar sun hada da mutane 18 a PDP, 12 APC. Daga ciki akwai mata 6 da maza kusan 30

Abuja - Bayan Farfesa Yemi Osinbajo ya ayyana burin takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, jaridar Vanguard ta ce masu neman takara sun kara yawa.

Daga cikin masu burin zama shugaban kasa akwai maza 29 da mata shida. A cikin matan, har da Nonye Josephine Ezeanyaeche mai shekara 102 a Duniya.

Rahoton da aka fitar a ranar Litinin, ya nuna cewa akwai akalla mutane 35 da su ke da niyyar shiga takarar shugaban kasar Najeriya a zaben da za ayi a 2023.

Kara karanta wannan

Atiku, Saraki da Tambuwal sai sun dage, ‘Yan takarar Kudu sun hada-kan su a PDP

Akalla mutum 30 daga cikin wadanda su ke sha’awar takara a zaben 2023 sun fito ne daga manyan jam’iyyun siyasan da ake ji da su a yau; PDP da APC.

'Yan takarar 2023 a jam'iyyu

Jam’iyyar African Democratic Congress ta na da ‘yan takara biyu, jam’iyyun APGA, SDP da PRP duk su na da mutum guda da ke neman mulki zuwa yanzu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda za su gwabza wajen neman tikitin jam’iyyar ADC a zabe mai zuwa su ne Farfesa Kingsley Moghalu da kuma Chukwuka Monye mai shekara 42.

Tinubu da Buhari a Aso Villa
Asiwaju Tinubu da Shugaban kasa Hoto: @Bashir Ahmaad
Asali: Facebook

Matan da za su nemi yin takara

Rahoton ya ce matan da suka bayyana burin tsayawa takara su ne; are Khadijah Okunnu-Lamidi (SDP); Ibinabo Joy Dokubo (APC); sai Patience Key (PRP).

Sai Olivia Diana Teriela da za ta jarraba sa’arta a jam’iyyar PDP; da kuma Angela Johnson a APGA. Baya ga Madam Nonye Josephine Ezeanyaeche kenan.

Kara karanta wannan

Tsadar fom din takara: Ana son hana matasa mulki a Najeriya, inji wani dan takaran APC

Yakin tikitin jam'iyyar PDP

A cikin manyan masu neman takara a PDP akwai; Atiku Abubakar, Dr Bukola Saraki, Gwamna Nyesom Wike, Aminu Waziri Tambuwal da Bala Mohammed.

Sai Udom Emmanuel, Ayodele Fayose, Muhammed Hayatu-Deen, Anyim Pius Anyim, Peter Obi, Dele Momodu, Sam Ohuabunwa da Nwachukwu Anakwenze.

Masu neman tutan APC a 2023

A jam’iyyar APC za a buga ne tsakanin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Yemi Osinbajo, Rochas Okorocha, Dave Umahi, Alhaji Yahaya Bello da Orji Uzor Kalu.

Sannan akwai Rotimi Amaechi, Tunde Bakare, Ihechukwu Dallas Chima, Moses Ayom da sauransu.

Ya kamata a ba 'Yan kudu mulki?

A makon da ya wuce labari ya zo mana cewa manyan ‘Yan siyasar Kudu maso gabas sun yi zimma wajen ganin Ibo ya samu takarar shugaban kasa a PDP.

Anyim Pius Anyim da Peter Obi za su yi koyi da abin da Bukola Saraki ya zo da shi na fito da ‘Dan takara daya daga shiyya domin Ibo ya zama shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Kwankwaso ya koma NNPP, ta yiwu Tinubu kuma ya koma SDP, inji majiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel