Bayan harin Filato, yan bindiga sun sake kashe mutum 19 a wata jihar arewa

Bayan harin Filato, yan bindiga sun sake kashe mutum 19 a wata jihar arewa

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun farmaki wasu garuruwa a jihar Benue inda suka hallaka mutane 19 da basu ji ba basu gani ba
  • Faruwar lamarin ya sanya matasa yin zanga-zanga a babban titin Makurdi zuwa Gboko inda suka jibge gawarwakin mutanen da harin ya ritsa da su
  • Hadimin gwamnan jihar, James Igbudu, ya tabbatar da lamarin sannan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta baiwa al'ummarsa kariya daga yan bindiga

Benue - Jaridar The Nation ta rahoto cewa yan bindiga sun kashe akalla mutane 19 a wasu garuruwan jihar Benue.

An tattaro cewa yan bindigar sun farmaki garin Tyiortyu na karamar hukumar Mbakor Tarka, inda suka kashe mutane 10.

A safiyar ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, wasu fusatattun matasa sun toshe babban titin tarayya da kan kasance cunkus da mutane daga Makurdi, babbar birnin jihar zuwa Gboko domin yin zanga-zanga a kan lamarin.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe

Bayan harin Filato, yan bindiga sun sake kashe mutum 19 a wata jihar arewa
Bayan harin Filato, yan bindiga sun sake kashe mutum 19 a wata jihar arewa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Toshewar ya yi sanadiyar tsayar da harkoki yayin da zirga-zrgan ababen hawa ya tsaya cak tsawon sama da awowi 10.

Garin Tyortyu birni ne da ke kan babbar hanyar Makurdi zuwa Gboko a cikin karamar hukumar Tarka a jihar Benue.

Wani mazaunin garin da ya tsallake rijiya da baya a harin, Tersoo Utume, ya fada ma The Nation cewa yan bindigar sun farmaki yankin da misalin karfe 2:00 na tsakar daren Talata inda suka bi gida-gida, suna ta harbin mazauna kauyukan da basu ji ba basu gani ba.

Matasan garin sun ajiye gawarwaki a kan babbar titin tarayyan.

A kauyen Tse-Sumaka, yan bindiga sun kashe manoma tara a kusa da Umenger da ke yankin Mbadwem a karamar hukumar Guma a ranar Litinin.

Babban mai ba Gwamna Samuel Ortom shawara kan harkokin labarai, James Igbudu, wanda ya tabbatar da kashe-kashen, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta baiwa garinsa kariya daga yan bindiga.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da motoci biyu na matafiya a jihar Ribas

Kakakin yan sandan Benue Kate Aneene, SP, ta ce tana a hanyarta ta zuwa wajen da abun ya afku tare da kwamishinan yan sanda kuma za ta yi jawabi bada jimawa ba.

An kashe mutane masu yawan gaske yayin da yan bindiga suka farmaki kauyukan Filato 4

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa yan bindiga sun farmaki kauyuka hudu a yankin karamar hukumar Kunam da ke jihar Filato a safiyar ranar Lahadi, 10 ga watan Afrilu.

An tattaro cewa harin wanda ya wakana a garuruwan Kukawa, Gyanbahu, Dungur da Keram, ya yi sanadiyar mutuwar mutane da yawa.

Jaridar Vanguard ta kuma rahoto cewa an tabbatar da mutuwar fiye da mutum 70 a harin na ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel