Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da motoci biyu na matafiya a jihar Ribas

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da motoci biyu na matafiya a jihar Ribas

  • Yan bindiga sun kai farmaki kan wasu motoci biyu shake da fasinjoji a jihar Ribas inda suka yi awon gaba da su zuwa wani waje da ba a sani ba
  • Wannan al'amari da ya afku a yammacin jiya Litinin, 11 ga watan Afrilu, ya saka tsoro da fargaba a zukatan al'umman yankin
  • Zuwa yanzu ba a ji ta bakin rundunar yan sandan jihar Ribas a kan lamarin ba, amma wasu mazauna jihar sun tabbatar da faruwan sa

Rivers - Rahotanni sun kawo cewa wasu tsagerun yan bindiga sun sace wasu motocin bas guda biyu dauke da fasinjoji a jihar Ribas.

An tattaro cewa motocin na a hanyarsu ta zuwa yankin Kalabari a kananan hukumomin Degema, Asaritoru da Akukutoru daga Port Harcourt, inda aka tsare su a hanyar Degema/Buguma/Abonnema.

Kara karanta wannan

Bayan harin Filato, yan bindiga sun sake kashe mutum 19 a wata jihar arewa

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da motoci biyu na matafiya a jihar Ribas
Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da motoci biyu na matafiya a jihar Ribas Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Lamarin ya afku ne a yammacin ranar Litinin, 11 ga watan Afrilu, jaridar The Nation ta rahoto.

Zuwa yanzu rundunar yan sandan Ribas bata tabbatar da lamarin ba amma mazauna yankin sun ce lamarin ya haddasa fargaba a cikin yankin.

Rahoton TVC News ya kuma kawo cewa har yanzu ba a san inda fasinjoji da motocin suke ba.

Batun ra shin tsaro: Tsohon ministan Buhari ya yiwa shugaban kasar wankin babban bargo

A wani labarin, tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gazawa yan Najeriya sannan cewa ya baiwa mutane da dama kunya ciki harda shi saboda ya kasa magance matsalar rashin tsaro a kasar.

Dalung ya bayyana hakan ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 10 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe

Tsohon ministan ya kuma koka kan cewa shugaban kasar na raba iko tare da kasurgumin shugaban yan bindiga na arewa maso yamma, Bello Turji da kuma mayakan ISWAP sakamakon gazawarsa wajen magance rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel