Ba halinmu bane: Rundunar 'yan sanda ta kamo jami'in da aka ga yana busa tabar wiwi a bainar jama'a

Ba halinmu bane: Rundunar 'yan sanda ta kamo jami'in da aka ga yana busa tabar wiwi a bainar jama'a

  • Hukumomin ‘yan sanda a jihar Legas sun kama wani jami’in da aka gani a wani faifan bidiyo yana busa wiwi a bainar jama'a
  • Jami’in da ke aiki a daya daga cikin sassan ‘yan sanda a jihar Legas yanzu haka dai zai fuskanci matakin ladabtarwa daga hukumarsu
  • Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya dama ya bayar da umarnin cafke jami’in nan take bayan ganin faifan bidiyonsa a shafin Twitter

An kama wani ASP na ‘yan sanda dake aiki da sashen Shogunle da ke Legas, Babatunde Adebayo, da laifin shan tabar wiwi a bainar jama’a, inji rahoton Daily Trust.

An dauki Adebayo a kyamara lokacin da yake busa hayakin tabar wiwi yayin da yake cikin wani taro a ranar Lahadi, 10 ga Afrilu.

Kara karanta wannan

Watan Ramadan: 'Yan Sandan Kano Sun Hana Yin 'Tashe' a Jihar, Sun Bada Dalili

Rundunar 'yan sanda ta kama jami'in ta da ke shan wiwi
Ba halinmu bane: Rundunar 'yan sanda ta kamo jami'in da aka ga yana busa taba a bainar jama'a | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

A wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, kakakin rundunar ‘yan sanda, SP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa:

“Kwamishanan ‘yan sandan jihar Legas, CP Abiodun Alabi, ya bayar da umarnin a fara aiwatar da matakan ladabtar da shi cikin gaggawa da suka dace da matsayinsa.”

Kakakin hedikwatar ‘yan sanda ya tabbatar da kama jami’in

Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar sanda, Prince Olumuyiwa Adejobi, shi ma ya tabbatar da kama jami'an a wani sako da ya wallafa a shafin Twitter.

A wani sakon da ya wallafa a shafin Twitter, Prince Adejobi ya rubuta cewa:

“Mafi rinjaye, halayen rashin da'a suna faruwa ne ta dalilin shan muggan kwayoyi da kuma amfani da su ba daidai ba, har ma wasu ayyuka mara kyau da jami’an tsaro ke yi dalilin shan miyagun kwayoyi ne. Don haka za mu gargade su kafin su yi kuskure ko fiye da haka. Ku yi abin da ya dace a lokacin da ya dace.”

Kara karanta wannan

Ashe makiyaya ne ba ‘Yan bindiga ba – ‘Yan Sanda sun yi karin haske kan bidiyon da ke yawo

Za mu kwamushe shi: Za a yi maganin wani dan sandan da aka ga yana busa taba a bainar jama'a

A tun farko, wani dan sanda da aka kama yana busa taba a bainar jama'a, zai iya shiga cikin babbar matsala idan har abin da 'yan sandan Najeriya ke fada ya zama gaskiya.

An ga dan sandan a cikin wani hoto a cikin kwanciyar hankali yana jin dadin rayuwarsa ta hanyar busa hayaki sama a bainar jama'a sanye da cikakken kayan aikinsa.

Bai sani ba, wani ya dauki hotonsa ya aika wa shugabanninsa kuma hukumomin suka ce yanzu haka suna nemansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel