Za mu kwamushe shi: Za a yi maganin wani dan sandan da aka ga yana busa taba a bainar jama'a

Za mu kwamushe shi: Za a yi maganin wani dan sandan da aka ga yana busa taba a bainar jama'a

  • Hukumomin ‘yan sanda sun sha alwashin kamawa tare da yin maganin wani dan sanda da ba a bayyana sunansa ba, wanda aka kama yana busa taba a bainar jama’a
  • Wani hoto da aka gani a shafin Twitter ya nuna cewa mutumin yana zaune ne cikin kwanciyar hankali yana busa taba sanye da kakin 'yan sanda
  • Sai dai shugabannin sa sun ce ba za su lamunta ba kuma sai sun dauki kwararan matakan ladabtarwa a kan jami’in da ya yi kuskuren bata sunan 'yan sanda

Wani dan sanda da aka kama yana busa taba a bainar jama'a, zai iya shiga cikin babbar matsala idan har abin da 'yan sandan Najeriya ke fada ya zama gaskiya.

An ga dan sandan a cikin wani hoto a cikin kwanciyar hankali yana jin dadin rayuwarsa ta hanyar busa hayaki sama a bainar jama'a sanye da cikakken kayan aikinsa.

Kara karanta wannan

Innalillahi wa’inna illahi raji’un: Allah ya yiwa sajan Funtua wanda harin jirgin kasa ya cika da shi rasuwa

Hukumar 'yan sanda kan wani dan sandan da ya bata masu suna
Za mu kwamushe shi: Za a yi maganin wani dan sandan da aka ga yana busa taba a bainar jama'a | Hoto: @policeng and @Princemoye1
Asali: Twitter

Hotonsa ya karade kafafen sada zumunta

Bai sani ba, wani ya dauki hotonsa ya aika wa shugabanninsa kuma hukumomin suka ce yanzu haka suna nemansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin wani sakon Twitter, Prince Olumuyiwa Adejobi, mukaddashin rundunar 'yan sanda a Abuja ya ce:

“’Yan sanda sun fara daukar matakin da ya dace kan wannan mummunan yanayi. Mun tuntubi rundunar ‘yan sandan Legas domin su kwamuso shi, su bayyana sunansa kuma su kunyata shi, kuma za a dauki matakin ladabtarwa daga ofishin IGP nan take.
“An yi Allah wadai da wannan lamari gaba daya domin ba halin ‘yan sanda bane ne, abin takaici ne yadda muka ga jami’in ‘yan sanda sanye da kayan aikinsa ya lalata sunansa zuwa wannan mataki. Dole ne mu tauna tsakuwa domin mu tsarata aya. Mun gode, MUYIWA Adejobi."

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Bidiyon busasshen tsohon da mutuwa ta mance dashi ya girgiza intanet

Martanin 'yan soshiyal midiya

'Yan Najeriya a shafin Twitter sun mayar da martani a sashin sharhi don bayyana ra'ayoyinsu kan wannan yunkuri na 'yan sanda.

Ga kadan daga maganganun jama'a:

@Princemoye1 ya bayyana yadda 'yan sandan na Najeriya ke yin biris da kin cika alkawuran da suka dauka, inda yace:

"Kwanaki 27 da suka gabata kuka yi wannan rubutu har ma da alkawari. Babu bayani guda daya tun daga lokacin. Don Allah me yasa zamu yarda da ku akan wannan?"

@Ngozichuwku ya ce:

"Yi tunanin ganin likita yana son yi maka aiki da taba a hannunsa?? Za ka barshi ya cigaba da aikin??"

@Princemoye1 ya ce:

"Irin mutanen da 'yan sanda ke bari su shiga cikin ma'aikatansu abin nuna damuwa ne."

Budurwa ta danna wa tsohon saurayinta wuka har lahira kan kyautar N3,000

A wani labarin, rundunar yan sanda reshen jihar Legas ta damƙe wata budurwa yar shekara 26, Oluwatoyin Joshua, bisa zargin sheƙe tsohon saurayinta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malaysia za ta daure ko cin tarar 'yan kasa da ke cin abinci da rana a Ramadan

Tribune Online ta rahoto cewa ana zargin matashiyar ta sheke saurayin ne kan kyautar N3,000 a yankin Shangisa dake cikin Legas.

Jami'i mai zana hotuna na hukumar, Adekunle Ajisebutu, a madadin kwamishinan yan sanda, ya ce wani mai kyakkyawan niyya ne ya ba su kyautar kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel