Sabon hari: An kashe sabon sarkin gargajiya a yankin Kaduna, da wasu mutum 14

Sabon hari: An kashe sabon sarkin gargajiya a yankin Kaduna, da wasu mutum 14

  • Wani sabon mummunan hari ya sake faruwa a Kaduna, inda wasu 'yan bindiga suka hallaka wani basaraken gargajiya
  • Lamarin ya haifar da hargitsi, inda matasa daga yankin suka kai hari mai kama da na daukar fansa kan Fulani
  • Ya zuwa yanzu dai hukumomin tsaron jihar Kaduna basu yi martani ba kan wannan mummunan lamari

A ranar Lahadi ne al’ummar Kakura da ke karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna ta shiga tashin hankali, biyo bayan kisan da aka yi wa shugabansu Isiaku Madaki, lamarin da ya kai ga mutuwar wasu mutane 14 daban.

Kakura gari ne na al'ummar Gbagyi da ke da tarin sauran mazauna, kamar yadda Punch ta ruwaito.

An tattaro cewa an nada Madaki a matsayin shugaban al’ummar Kakura ne a ranar Asabar din jiya, kana a ranar Lahadi wasu ‘yan bindiga suka kashe shi.

Kara karanta wannan

Bauchi: An Kama Mai Hidimar Ƙasa Na Bogi Ya Saci Wayoyi a Sansanin NYSC

Barnar 'yan bindiga a Kaduna
Sabon hari: An kashe sabon sarkin gargajiya a yankin Kaduna, da wasu mutum 14 | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Lamarin ya haifar da wani hari da aka kai a wani matsugunin Fulani da ke yankin inda ake fargabar mutane 14 sun mutu.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi lokacin da Kiristoci ke shirin yin hidimar ibadarsu ta ranar Lahadi.

Yadda lamarin ya faru

Wani mazaunin garin mai suna Baban David ya bayyana cewa, an nada marigayin a matsayin shugaban al’ummar ne a ranar Asabar.

Ya ce:

“Dukkanmu mun taru a gidansa da sanyin safiyar (Asabar) domin mu taya shi murna kan nadin da aka masa. Mun yi mamaki da sanyin safiyar yau (Lahadi) muka fara jin karar harbe-harbe.
“Mun ji tsoro kuma ba mu iya fitowa daga gidajenmu ba. Daga baya kuma aka shaida mana cewa ‘yan bindigar sun kashe shi a gaban matarsa da iyalansa.

Kara karanta wannan

Bayan harin Tsafe, jami’an tsaro sun bankado maboyar yan bindiga a Zamfara

“Mun tarar da gawarsa kwance a kasa. Matarsa ta shaida mana cewa ‘yan bindigar sun kutsa cikin gidansu ne inda suka harbe shi. Ba su dauki komai ba, ba su kuma sace kowa ba.”

Kashe shugaban ya kai ga kai hari kan Fulani

A nasa bangaren, wani mazaunin garin mai suna Mallam Buhari ya bayyana cewa da sanyin safiyar yau Lahadi fusatattun jama'a sun farmaki matsugunan Fulani da ke kusa, inda ya bayyana su a matsayin munafukai, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Buhari ya ce yayin da suke barin yankin, an kai musu farmaki tare da kashe wasu daga cikinsu, ya kara da cewa:

“A kan hanyarmu ta fitowa daga kauyen mun kirga gawarwaki hudu. Daga baya a kan hanyar daji, an ga gawarwakin wasu goma a jibge a kasa.”

Ya batun yake daga bakin 'yan sanda da matakin da suke dauka?

A halin da ake ciki, an ce an baza ‘yan sanda a cikin al’umma domin tabbatar da doka da oda. Ko da al’amura sun koma daidai ga al’ummar, yawancin mazauna yankin sun kaurace wa yankin saboda fargabar abin da ka iya biyo baya.

Kara karanta wannan

Ana maganar rufe Majalisa domin tursasa Shugaban kasa ya tashi-tsaye kan lamarin tsaro

Gwamnatin jihar ko hukumar ‘yan sandan jihar ba su mayar da martani kan lamarin ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar, Mohammed Jalige, bai amsa kiran waya ba, bai kuma dawo da sakon tes ba.

Yan bindiga sun bindige shugaban Miyetti Allah a Abuja

A wani labarin, 'yan bindiga sun farmaki yankin Gwagwalada da ke Abuja, inda suka bindige shugaban kungiyar Miyetti Allah na yankin, Adamu Aliyu, har lahira.

An tattaro cewa yan bindigar sun kashe Adamu Aliyu ne tare da wasu mutane hudu a kusa da kauyen Daku a gudunmar Dobi da ke yankin a ranar Alhamis.

Daily Trust ta rahoto cewa sakataren kungiyar MACBAN, Mohammed Usman, wanda ya tabbatar da lamarin a ranar Lahadi, ya ce an yi garkuwa da mutane uku, yayin da wasu uku da suka jikkata ke karban magani a asibitin koyarwa na Gwagwalada.

Kara karanta wannan

Karar kwana: 'Yan bindiga sun kai hari Zamfara, sun kashe mutane da dama ciki har da hakimin kauye

Asali: Legit.ng

Online view pixel