Yadda cikin sati 2 Buhari ya magance matsalolin APC yayin da rashin tsaro ke cigaba

Yadda cikin sati 2 Buhari ya magance matsalolin APC yayin da rashin tsaro ke cigaba

  • 'Yan Najeriya sun caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda ya shawo kan matsalar APC cikin makonni 2 kacal amma ya gaza kan tsaro
  • An yi gagarumin taron jam'iyyar na kasa a ranar 26 ga watan Maris, yayin da jam'iyyar ke haramar rushewa sakamakon rikicin cikin gida
  • A wannan lokacin, 'yan ta'adda na cigaba da cin karensu babu babbaka a arewa yayin da matsalar man fetur da wutar lantarki ta yi kamari

FCT, Abuja - 'Yan Najeriya na cigaba da maganganu kan yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da hankali tare da shawo kan matsalar jam'iyyarsa a APC ana dab da yin gagarumin gangamin zaben shugabannin jam'iyyar na kasa.

Gangamin jam'iyyar da aka yi a ranar 26 ga watan Maris a Eagle Square an yi shi ne yayin da ake buga kugen rikicin cikin gida na jam'iyyar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya zasu zabi APC a 2023 saboda gwamnati na ta yi namijin kokari, Shugaba Buhari

Yadda cikin sati 2 Buhari ya magance matsalolin APC yayin da rashin tsaro ke cigaba
Yadda cikin sati 2 Buhari ya magance matsalolin APC yayin da rashin tsaro ke cigaba. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Har ila yau, an yi gagarumin taron ne yayin da kashe-kashe, satar jama'a da sauran lamurran kungiyoyin ta'addanci suka yi kamari a jihohin Kaduna, Niger da sauran wurare a fadin kasa nan.

Baya ga kalubalen tsaron, 'yan Najeriya na gwagwarmaya da wasu matsalolin tattalin arziki da suka hada da rashin wuta wanda ya kusa gurgunta dukkan sauran lamurran kasar da kuma rashin man fetur.

'Yan Najeriya sun dinga caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan halin ko in kula da ya nuna duk da zamansa ministan man fetur na kasa.

Yadda ka yi gangamin jam'iyyar yasa 'yan Najeriya tambayar ko shugaban kasa Buhari da gaske yake da ya ce gwanmnatinsa ta bai wa tsaron kasa fifiko a kan komai.

Daily Trust ta ruwaito cewa, jam'iyyar mai mulki ta fada rikicin cikin gida a lokacin da 'yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka a jihohin Niger, Kaduna da wasu jihohin arewa maso yammaci.

Kara karanta wannan

Buhari ya gaza, kuma bai shirya magance matsalar rashin tsaro ba, inji Sanata mai ci

Sai dai, da gaggawa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi amfani da isarsa na zama shugaban tare da hana jam'iyyar watsewa duk kuwa da matsalar tsaro da sauransu da ke bukatar irin wannan kulawar a kasar nan.

Ku ƙara ba jam'iyyar APC wata dama a 2023, Ahmad Lawan ya roƙi yan Najeriya

A wani labari na daban, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya roƙi yan Najeriya su taimaka wa jam'iyyar APC da wata dama a 2023, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Lawan ya yi wannan rokon ne a wurin taron tattaunawa da Sanatan Kwara ta tsakiya, Dakta Ibrahim Yahaya Oloriegbe, ya shirya ranar Asabar.

A wurin taron wanda ya gudana a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, Oloriegbe, ya bayyana aniyar zarcewa a kujerarsa karo na biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel