Ku ƙara ba jam'iyyar APC wata dama a 2023, Ahmad Lawan ya roƙi yan Najeriya

Ku ƙara ba jam'iyyar APC wata dama a 2023, Ahmad Lawan ya roƙi yan Najeriya

  • Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya roki yan Najeriya su sake ba APC dama a babban zaɓen 2023
  • Lawan, ya ce APC ta ɗauki alƙawarin zata cigaba da yin iya bakin kokarinta kuma zata ɗora daga kan inda ta tsaya
  • Sanatan ya kuma gargaɗi al'umma cewa ka da su sake kuskuren zaɓen PDP domin ba zasu gaji da neman dawowa mulki ba

Kwara - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya roƙi yan Najeriya su taimaka wa jam'iyyar APC da wata dama a 2023, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Lawan ya yi wannan rokon ne a wurin taron tattaunawa da Sanatan Kwara ta tsakiya, Dakta Ibrahim Yahaya Oloriegbe, ya shirya ranar Asabar.

A wurin taron wanda ya gudana a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, Oloriegbe, ya bayyana aniyar zarcewa a kujerarsa karo na biyu.

Kara karanta wannan

Ba na shakkan Tinubu ko Osinbajo, duk zan kada su - Yahaya Bello

Shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan.
Ku ƙara ba jam'iyyar APC wata dama a 2023, Ahmad Lawan ya roƙi yan Najeriya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Tun ɗa farko, Lawan ya kaddamar da fara aikin gyara a wani Asibitin tarayya a Budo-Egba, Karamar Hukumar Asa, daga bisani ya kaddamar da wani Asibiti a yankin Okolowo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban majalisan ya kuma gargaɗi al'ummar jihar kan kuskuren komawa gidan jiya wato mulkin PDP a jiharsu.

Ya faɗa wa mahalarta taron cewa namijin kokarin da Oloriegbe ya yi daga zuwansa majalisa ya zarce na dukkan waɗan sa suka rike kujerar Sanata kafin shi a mazaɓar.

Tsohon shugaban majalisa, Bukola Saraki, na ɗaya daga cikin waɗan da suka wakilci mutane a mazaɓar kafin zuwan Oloriegbe.

Lawan ya ce:

"Ina so na yi kira ga yan Najeriya su sake ba jam'iyyar APC dama a kowane mataki a 2023. Mun yi wa yan Najeriya alƙawari zamu cigaba da yin bakin kokarin mu, zamu tsaya tsayin daka kan alƙawarin mu."

Kara karanta wannan

Shin da gaske Shugaba Buhari ya sake shillawa Landan ganin Likita?

Kada ku sake amince wa da PDP - Lawan

Lawan ya kuma ƙara da cewa ka da mutane su ƙara yin kuskuren dawo da hannun agogo baya, su sake yarda da jam'iyyar PDP.

"Ina tunatar da ku cewa waɗan can mutanen da kuka kora ba zasu gaji da faɗi tashin dawowa ba. Har yanzun akwai sauran ku a tafiyar "Otoge" kada ku bari su dawo."

A wani labarin kuma Daga Ƙarshe, Ministan Buhari ya ayyana shiga tseren takarar shugaban ƙasa a 2023

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana aniyarsa ta gaje Buhari a zaɓen 2023 dake tafe karkashin APC.

Tsohon gwamnan jihar Ribas ya ayyana kudirinsa a ranar Asabar a Filin wasa na Adokiye Amiesimaka Stadium dake jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel