Wani Matashi Ɗan Shekara 33 Ya Haura Gidan Obasanjo, Ya Yi Yunƙurin Yi Wa Tsohon Shugaban Ƙasar Sata

Wani Matashi Ɗan Shekara 33 Ya Haura Gidan Obasanjo, Ya Yi Yunƙurin Yi Wa Tsohon Shugaban Ƙasar Sata

  • Seun Sowemimo zai kwashe shekara daya cur a gidan gyaran hali bayan ya yi yunkurin sata a gidan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo
  • An samu bayanai akan yadda Sowemimo, mai shekaru 33 ya haura katangar gidan Obasanjo da ke Abeokuta inda ya dira harabar gidan da niyyar yin sata
  • Yayin da ya bayyana a kotu, matashin ya amsa laifuka biyun da ake zarginsa da su, na sata da kuma tayar da hankali kuma zai yi watanni 12 a gidan yari babu zabin biyan tara

Ogun - Wata kotun majistare da ke zama a Abeokuta a ranar Juma’a, 8 ga watan Afirilu ta yanke wa wani Seun Sowemimo, mai shekaru 33 watanni 12 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba bayan ya yi yunkurin yi wa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo sata.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Bidiyon busasshen tsohon da mutuwa ta mance dashi ya girgiza intanet

Sowemimo ya amsa laifuka biyu da ake zarginsa da aikatawa na sata da kuma tayar da hankali kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kotu Ta Ɗaure Matashin Da Ya Haura Gidan Tsohon Shugaban Ƙasa, Obasanjo Ya Yi Ƴunƙurin Sata
Kotu Ta Ɗaure Matashin Da Ya Haura Gidan Tsohon Shugaban Ƙasa, Obasanjo Ya Yi Ƴunƙurin Sata
Asali: Getty Images

Legit.ng ta tattaro cewa alkalin majistaren, Mrs Olajumoke Somefun, ta ce an yanke hukunci ne bisa samun tabbaci akan cewa Sowemimo ne ya aikata laifukan.

Wani mai gadi ne ya kama Sowemimo yana yunkurin sata

Mai gabatar da kara, ASP Olakunle Shonibare, tunda farko ya bayyana wa kotu yadda mai laifin ya haura katanga inda ya dira harabar gidan Obasanjo da ke Abeokuta a ranar Juma’a, 1 ga watan Afirilu da niyyar yin sata, The Punch ta ruwaito.

Ya yi bayani akan yadda yana dirawa wani jami’in tsaron gidan ya kama shi.

A cewar Shonibare, laifin ya ci karo da dokar masu laifi ta Ogun ta shekarar 2006.

Kara karanta wannan

Mubarak Bala: Martanin 'yan Najeriya kan hukuncin shekaru 24 da kotu ta yanke wa mulhidi

Kano: An cafke mai wankin mota da ya tsere da motar kwastoma ta N8.5m zuwa Katsina

A wani labarin, an kama wani mai aiki a wurin wankin mota a Kano, Abdullahi Sabo, saboda tsere wa da motar kwastoma da aka kawo masa wanki, Premium Times ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya ce an kama wanda ake zargin ne a Daura, Jihar Katsina da motar na sata.

Mr Kiyawa ya ce, a ranar 30 ga watan Nuwamba, yan sanda sun samu korafi daga wata mazauniyar Badawa Quaters a Kano inda ta ce wani mai aiki a wurin wankin mota ya gudu masa da motarsa Honda Accord ta shekarar 2017.

Asali: Legit.ng

Online view pixel