Mubarak Bala: Martanin 'yan Najeriya kan hukuncin shekaru 24 da kotu ta yanke wa mulhidi

Mubarak Bala: Martanin 'yan Najeriya kan hukuncin shekaru 24 da kotu ta yanke wa mulhidi

  • Yanke wa Mubarak Bala hukuncin shekaru 24 a gidan gyaran hali da wata kotun Kano ta yi a ranar Talata ya janyo cece-kuce
  • A tsokacin jama'a daga kudancin Najeriya, sun dinga mamakin yadda za a yanke masa hukunci da dokar addinin da bai yi imani da shi ba
  • Sai dai jama'ar arewacin Najeriya sun bayyana cewa an yi masa sassauci domin kuwa hukuncin kisa ya dace da shi ba daurin shekaru 24 ba

Mubarak Bala, mulhidi kuma haifaffen jihar Kano a ranar Talata an yanke masa hukuncin shekaru 24 a gidan yari.

Wata kotun jihar Kano ta yanke wannan hukuncin bayan ya amsa dukkan laifuka 18 da ake tuhumarsa da su.

Bala wanda shi ne shugaban Humanist Association of Nigeria, ya shiga hannun hukuma ne a ranar 28 ga watan Afirilun 2020 inda 'yan sanda suka bi shi har gidansa da ke Kaduna suka kama shi tare da mayar da shi jihar Kano.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke magidanci da bindiga, carbin harsashi 20, shanu 31 da tumaki 28 a Bauchi

Hakan ta faru ne bayan wata wallafa da yayi a shafinsa na Facebook wanda ya bayyana kalaman batanci game da Musulunci, Allah da Annabinsa kuma hakan ya janyo cce-kuce.

Mubarak Bala: Martanin 'yan Najeriya kan hukuncin shekaru 24 da kotu ta yanke wa mulhidi
Mubarak Bala: Martanin 'yan Najeriya kan hukuncin shekaru 24 da kotu ta yanke wa mulhidi. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Bala wanda ya kasance yana janyo cece-kuce a shafukan sada zumuntar zamani, tun bayan da ya bar Musulunci kuma ya bayyana akidarsa ta mulhidanci, ya saba wallafa masu tada kura.

A wani lokaci a 2014, lokacin da ya fara bayyana akidarsa ta mulhidanci, iyayensa sun mika shi asibitin mahaukata da ke Kano, inda aka tabbatar da lafiyar kwakwalwarsa kalau.

Jama'a sun yi martani

Tun bayan da labarin ya bazu, 'yan Najeriya daga kudu zuwa arewaci suna ta bayyana ra'ayoyinsu game da wannan hukuncin.

Ga wasu daga cikin martanin jama'a:

Wani ma'abocin amfani da Twitter ya kalubalanci yadda mutumin da ya bar addini za a gurfanar da shi a gaban kotu kuma a yi amfani da dokokin addinin wurin yi masa hukunci.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Mubarak Bala wanda aka daure saboda batanci ga Annabi

"Wa ya gurfanar da shi? A karkashin wacce doka? A yi wa mutum hukunci da addinin da bai yarda da shi ba? Da haka wata rana za a yi wa Kirista hukunci da Shari'a kan batanci," @Luter_O yace.

Wani kuwa bayyanawa yayi cewa zama mulhidi bai kai ga a yanke wa mutum hukuncin zaman gidan yari ba.

@AlexanderKing… : “Da gaske? Wani abu yayi baya ga kin yarda da Ubangiji?"
@ZakariyyaIbrah7: “Dama hukuncin kisa aka yanke masa, domin abinda ya dace da shi kenan kamar yadda shari'ar Musulunci ta tanadar."

Kotu ta yankewa Mubarak Bala hukuncin shekaru 24 a gidan yari

A wani labari na daban, kotu ta yanke hukunci kan karar da aka shigar kan Shahararren matashin da ke ikirarin bai yarda da Allah ba, dan asalin jihar Kano, Mubarak Bala, ranar Talata, 5 ga Afrilu, 2022.

Wata babban kotun jihar Kano dake zamanta a Audu Bako Secretariat ta yanke masa hukuncin daurin shekaru ashirin da hudu a gidan gyaran hali bayan amsa laifukan da ake tuhumarsa da su.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu ta yankewa Mubarak Bala hukuncin shekaru 24 a gidan yari

Gabanin yanke masa hukunci, Mubarak ya bukaci kotu ta sassauta masa saboda bai aikata abubuwan da ake zarginsa da su ba don tada tarzoma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel