Buhari ya rufe iyaka: Kwastam sun kama tirelolin shinkafar waje 11 da lita 82,700 na fetur

Buhari ya rufe iyaka: Kwastam sun kama tirelolin shinkafar waje 11 da lita 82,700 na fetur

  • Rundunar yaki da fasa-kwabri ta hukumar kwastam ta Najeriya ta yi kamu, ta kama tirelolin shinkafar waje
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da hukumar ke ci gaba da yaki da ayyukan fasa-kwabri a yankunan kasar nan
  • Hakazalika, an kama lita 82,700 na man fetur duk da aka shigo dasu daga kasashen ketare ba bisa ka'ida ba

Hukumar kwastam, a jiya, ta ce ta kama akalla lita 82,700 na man fetur da kuma tireloli 11 na shinkafar fasa-kwabrin 'yar waje daga kasashen makwabta a wasu ayyuka daban-daban da tayi.

Hakan ya zo ne kamar yadda hukumar NCS, reshen jihar Kebbi, ta ce ta kama haramtattun kayayyaki da darajarsu ta kai miliyan 87.7, Leadership ta ruwaito.

Da yake jawabi a taron manema labarai jiya a Legas, Shugaban Hukumar Kwastam na sashin, Hussein Ejibunu, ya ce an kama kwali 20 da kwalaben magungunan da ba a yi wa rajista ba, da kuma tarin daskararrun kaji 2,150 a Legas da Ogun.

Kara karanta wannan

Ramadana: Yin azumi na karawa mutum karfi da lafiyar jiki – In ji kwararriyar likita

Kwastam sun yi babban kamu
Hukumar Kwastam ta kama Lita 82,700 na fetur da Motoci 11 na Shinkafa na Kasar waje | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Ejibunu, ya kuma kara da cewa, an kwace kayayyakin da aka yi fasa-kwabrinsu da kudinsu ya kai jimillar kudin haraji (DPV) na Naira miliyan 767.6 a cikin watan Maris din 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, ya bayyana cewa, ya damu kan harin da ‘yan fasa-kwabri ke kai wa jami’an kwastam, yana mai cewa hakan ba zai hana rundunar ta shiga ayyukan yaki da fasa-kwabri ba.

Ya kara da cewa, za a ci gaba da karfafa yaki da fasa-kwabri a ko da yaushe domin dorewar zaman lafiyar tattalin arziki da kuma hana shigo da kayayyaki masu hadari zuwa kasar ta kowace hanya ta yankin Kudu maso Yamma.

Jami'an Kwastam Sun Kama 'Ɗan Sanda' Da Mota Maƙare Da Haramtacciyar Shinkafa a Katsina

Hukumar Kwastam, NCS, reshen Jihar Katsina ta kama buhunan aya, shinkafar kasar waje da motocci da wasu kayayyakin da kudinsu ya kai N42.793m, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

Rundunar ta kuma ce ta kama wani da ake zargi, da ya yi ikirarin cewa shi dan sanda ne da buhunan shinkafa 25 da aka shigo da su ta haramtacciyar hanya.

Mukadashin kwantrola, DC Dalha Wada Chedi, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai, ranar Laraba a Katsina, yana cewa an yi kwacen ne daga 1 ga watan Fabrairu zuwa yanzu.

Chedi ya ce rundunar ta kwace buhunan aya 400, da kudinsa ya kai Naira miliyan 10 cikin wata babban mota DAF, da ya kamata a biya musu kudin haraji na N6.750m.

Hutu Hameed Ali ya tafi, baya cikin halin rashin lafiya, inji hukumar Kwastam

A wani labarin, hukumar kwastam na Najeriya, ta karyata rahoton kafar yada labarai da ke cewa shugabanta, Hameed Ali ya yanke jiki ya fadi a ranar Laraba sannan cewa an fitar da shi kasar waje don jinya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, 27 ga watan Maris, dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar kwatsam, mataimakin kwanturola, Timi Bomodi, Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

Ya bayyana cewa rahoton kanzon kurege ne, domin Ali yana cikin koshin lafiya sannan ya tafi hutu ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel