Ramadana: Yin azumi na karawa mutum karfi da lafiyar jiki – In ji kwararriyar likita

Ramadana: Yin azumi na karawa mutum karfi da lafiyar jiki – In ji kwararriyar likita

  • Yin azumi na taimakawa sassan jiki wajen samun hutu da tsarkake kansa
  • Wata kwararriyar likita kuma shugabar kungiyar likitoci mata ta Najeriya (MWAN), reshen Kwara, Dr Bilqis Alatishe-Muhammad, ce ta bayyana hakan
  • Alatishe ta ce kauracewa ci da sha yana taimakawa sosai wajen hana yawan kitse da cutattuka masu alaka a jikin dan adam

Kwara - Dr Bilqis Alatishe-Muhammad, shugabar kungiyar likitoci mata ta Najeriya (MWAN), reshen Kwara, ta bayyana cewa azumi na ba sassan jiki damar hutawa da kuma fitar da abubuwa masu cutarwa da kansu.

Alatishe ta fadama kamfannin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba a Ilorin cewa yayin da musulmai a fadin duniya ke yin azumin Ramadan, sassan jikinsu za su huta kuma za su ji karfin jiki.

Kara karanta wannan

Ziyarar Kaduna: Tinubu ya samu tabarraki daga wajen Sheikh Dahiru Bauchi

Ramadana: Yin azumi na karawa mutum karfi da lafiyar jiki – In ji kwararriyar likita
Ramadana: Yin azumi na karawa mutum karfi da lafiyar jiki – In ji kwararriyar likita Hoto: naijaloaded.com
Asali: UGC

A cikin watan Ramadan kowace shekara ta Musulunci, Musulmai a fadin duniya na kame bakinsu daga ci da sha ta hanyar yin azumi da jajircewa wajen addu’o’i da ibadah.

Hakazalika azumin Ramadana na daya daga cikin shika-shikan musulunci biyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin azumin, Musulmai na kauracewa tarayya ta auratayya, suna kame bakinsu daga ci da sha tun daga billowar alfijir har zuwa ga faduwar rana, inda hakan ke sa su kame kansu, sadaukarwa da kuma tausayawa na kasa da su.

Alatishe ta bayyana cewa ta hanyar kauracewa abinci da abun sha, sassan jiki na cire guba da kansa ta hanyar tsaftace hanta, hanji da kuma koda, da taimakon huhu da fata.

Ta bayyana cewa sassan jiki na tsaftace kansa, cewa:

“Hakan na faruwa ne da kansa ta hanyar azumi.
“Mutane na azumi ta hanyar kauracewa abinci da abun sha saboda dalilai na lafiya ko na addini.

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

“Kauracewar na iya zama cikakke ko kadan. Hakanan zai iya zama na dogon lokaci ko gajeren lokaci.
“A watan Ramadana, ana azumi daga billowar alfijir zuwa faduwar rana na kwanaki 29 ko 30.
“Guba a cikin jiki na iya haifar da illa. Don haka, tsaftace sassan jiki na hana yawan kitse da cututtuka masu alaka.
"Hakanan yana rage kumburi sannan kuma yana inganta aikin kwakwalwa."

Shugabar kungiyar ta MWAN ta bayyana cewa wasu masu bincike sun gano cewa azumi na iya daidaita sukarin jini ta hanyar rage sinadarin insulin, rahoton The Nation.

Ta kara da cewar: “Azumi na da kyau ga sassan jiki; yana kara lafiyar jiki.”

Ramadana: Yadda masu ciwon suga za su yi azuminsu cikin sauki

A gefe guda, wani kwararren likita mai suna Dr. Oluwarotimi Olopade, ya bukaci masu ciwon sukari na 2 da ke fatan yin azumi da su tattauna da likitocinsu kafin su fara.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyon Oshiomhole yana nuna kwarewarsa wurin rawa a bazdensa na 70

Wannan kira na Dr Olopade na zuwa ne a daidai lokacin da watan Ramadana ke kara karatowa, wanda a cikinsa Musulmi ke yin azumi na kwanaki 29-30.

Likitan wanda ya kuma kasance masanin ciwon suga a asibitin koyarwa na jami’ar Lagas, ya bayyana cewa akwai bukatar masu ciwon suga su zanta da likitocinsu don sanin ko sun cancanci yin azumi bisa ga matsayin lafiyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel