Nasrun minAllah: Boko Haram sun sheƙe kwamandojin ISWAP 10 a yankin tafkin Chadi

Nasrun minAllah: Boko Haram sun sheƙe kwamandojin ISWAP 10 a yankin tafkin Chadi

  • Boko Haram dake yankin tafkin Cadi sun ragargaji mayaƙan ISWAP, gami da sheke shugabanninsu 10, yayin wata musayar wuta tsakanin kungiyoyin ta'addancin biyu
  • Yayin gumurzun, an jefa mayaka da dama cikin ruwa, daga bisani Boko Haram na Budama suka kama mayakan ISWAP 10
  • Sun dau watannin muna rikici, a da kan turba daya suke, amma daga baya suka koma yakar juna ba tare da wani daliliba

Borno - A ƙalla mayaƙan ISWAP goma, duk da manyan kwamandojinsu suka rasa rayukansu yayin artabu da abokan hamayyarsu a ta'addancin, Jama'at Ahl as-Sunnah lid- Da'awah wa'l- Jihad, wani nau'in Boko Haram na arewa maso gabashiin tafkin Chadi suka kai musu farmaki.

Zagazola Makama, fitaccen mai bibiyar lamurran kungiyoyin ta'addancin ne ya bayyana hakan, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: Sojoji sun samu gagarumar nasara kan Boko Haram/ISWAP a wani gumurzu

Nasrun minAllah: Boko Haram sun sheƙe kwamandojin ISWAP 10 a yankin tafkin Chadi
Nasrun minAllah: Boko Haram sun sheƙe kwamandojin ISWAP 10 a yankin tafkin Chadi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda ya ce, ƴan Boko Haram na Buduma sun yi luguden wuta ga ISWAP, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mayakan da dama a bakin tafkin dake tsakanin iyakar Kaduna Ruwa da Kandahar na Jamhuriyar NIger.

An jefa mayaƙa da dama cikin ruwan, daga bisani ƴan Boko Haram na Budama suka kama mayaƙan ISWAP guda 10 bayan gumurzun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Vanguard ta ruwaito cewa, kwararren da wani jami'in tsaro na tafkin Chadi sun dauki bidiyon dake nuna yadda ƙungiyoyin ƴan ta'addan guda biyu suka yi musayar wuta a kan jirgin ruwa.

Haka zalika, a bidiyon da ya ɗauki tsawon awa 6:40 wanda Zagazola ya nada, an kama shugabannin ISWAP guda biyu, gami da musu yankar rago.

Babban shugaban kungiyar Budama, wanda ake zarginsa da zama Muhammad Ari, ƙasurgumin jagoran yaƙi, wanda ya bayyana a bidiyon, ya ce Ubangiji na cigaba da basu ikon samun nasara a kan maƙiyansu (ISWAP).

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin yaƙin Sojojin Najeriya ya halaka dandazon yan bindiga a bodar Kaduna da Neja

Ya ce: "Mu ne masu jahadi daga kungiyar Jama'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wa'l-Jihad na tafkin Cadi.
"Sanin kanku ne, an daɗe ana bata-kashi tsakaninmu da maƙiyanmu (ISWAP) sama da watanni da suka shuɗe, kuma Ubangiji na bamu nasara wajen kauda maƙiyanmu daga doron ƙasa.
"Mun kama kusan goma daga cikinsu duk da wasu daga cikin kwamandojinsu, sannan mun tambayesu dalilin da yasa suke yaƙarmu. Amma kwamandojin nasu sun ce basu da wani dalili, kawai dai suna yaƙarmu ne.
"To ko shugabannin ku da kuke bi a makance, sun ce basu san dalilin da yasa suke faɗa da mu ba, balle ku mabiyansu.
"A fari dai, muna yin abu iri ɗaya sannan muna tafiya kan turba daya kafin ku canza, gami da barin koyarwan Ubangiji, tare da aikata dukkan munanan abubuwa.
"Saboda haka, muna tabbatar muku da cewa Ubangiji zai cigaba da bamu nasara wajen gamawa da dukkan ku daga doron ƙasa."

Kara karanta wannan

Neja: Yadda Kwale-Kwale ya nutse da mata da kananan yara yayin guduwa daga harin yan bindiga

Zubda jinanai tsakanin kungiyoyin ƴan ta'addan biyu na cigaba da ƙamari musamman a iyakar tafkin Cadi, Abadam, Jamhuriyar Niger, dajin Sambisa da tsaunin Mandara tare da ritsawa da ɗaruruwan mutane, daga ɓangarorin guda biyu a shekarar da ta gabata.

"A ranar 24 da 28 na watan Maris, 2022, ƴan ta'addan JAS masu bin bayan Bakura Buduma, sun yi kwantan ɓauna gami da sheƙe ƴan ta'adda 45 a Yauma Wango da Ngaama, cikin ƙaramar hukumar Abadam na jihar Borno," a cewar kwararren.

Asali: Legit.ng

Online view pixel