Da Duminsa: Daga Komarwarsa NNPP, Kwankwaso Ya Samu Muhimmim Muƙami

Da Duminsa: Daga Komarwarsa NNPP, Kwankwaso Ya Samu Muhimmim Muƙami

  • An nada Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin jagoran jam'iyyar New Nigeria People's Party, NNPP, na kasa
  • Hakan na zuwa ne kwana guda bayan barin tsohuwar jam'iyyarsa ta Peoples Democratic Party PDP
  • An kuma nada wasu mukarraban Sanata Rabiu Kwankwaso a matsayin mambobin kwamitin NEC na jam'iyyar NNPP

A jiya, an naɗa tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin jagoran jam'iyyar New Nigeria People's Party (NNPP), The Nation ta ruwaito.

The Punch ta ruwaito cewa an amince da nadin Kwankwaso ne a wurin taron jam'iyyar a Abuja, kwana ɗaya bayan ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP a Abuja.

Daga Shigarsa Jam'iyyar, An Naɗa Kwankwaso Jagoran Jam'iyyar NNPP Na Ƙasa
Jam'iyyar, An Naɗa Kwankwaso Jagoran Jam'iyyar NNPP Na Ƙasa. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Mabiya tsohon gwamnan na Kano suma sun samu mukamai a kwamitin jam'iyyar na NEC mai mutane 39 da za su jagoranci harkokin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sabon Shugaban APC ya dira Sakatariyar jam'iyya ta ƙasa, ya kama aiki gadan-gadan

Farfesa Rufai Alkali, masanin kimiyyar siyasa kuma tsohon sakataren watsa labarai na PDP ne ya zama shugaban NNPP na ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Saura sun hada da Air Vice Marshall Ifemeje John Chris (Mataimakin Shugaban Jam'iyya na Kasa); Mr Dipo Olayoku (Sakatare na Ƙasa); Sanata Suleiman Hunkuyi (Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa) da Manjo Gilbert Agbo (Sakataren Watsa Labarai na Kasa) da sauransu.

Da ya ke jawabi a wurin taron, Kwankwaso ya ce ya gamsu da goyon bayan da magoya bayansa suka nuna.

Ya ce:

"Abin da ya rage mana shine mu koma ga talakawan, a jihohin mu da kananan hukumomi mu yi rajista da iyalan mu sannan mu fada wa yan Najeriya su yi rajista da NNPP.
"Dukkan mu mun san cewa mutane sun gaji da APC da PDP shi yasa mutane ba su fito sosai ba a zaɓen da ya gabata. Mun gode wa Allah cewa mun samu sabon Najeriya. Mutane sun gaji kuma suna son canji kuma NNPP ce sabuwar iska mai tsafta da za ta iya basu canjin."

Kara karanta wannan

Zaben APC: Goyon bayan Buhari, sanin siyasa da abubuwa 4 da suka taimakawa Adamu

Legit.ng Hausa ta tuntubi Kwamared Ibrahim Danlami Kubau, dan takarar kujerar majalisar dokoki na tarayya na mazabar Ikara/Kubau don jin ra'ayinsa game da shigowar Sanata Kwankwaso jam'iyyar NNPP da mukamin da aka bashi.

Kwamared Kubau ya ce shigowar Kwankwaso jam'iyyar NNPP alheri ne kuma ya cancani mukamin jagoran jam'iyyar na kasa.

Ya cigaba da cewa shi (Kwankwason) dan siyasa ne wanda ke da tarin magoya baya da masoya kuma ya dade yana yi wa mutane hidima duk da ba shi da mulki a hannunsa.

"Muna farin ciki da shigowar Kwankwaso wannan tafiyar domin shi mutum ne mai dumbin magoya baya da masoya kuma mai taimakon al'umma ta hanyoyi daban-daban misali daukan nauyin ilimin matasa a kasashen waje da gida Najeriya.
"Ra'ayin Kwankwaso na siyasa sun dace da manufofin jam'iyyar NNPP hakan yasa ya shigo tafiyar domin yan Najeriya sun gaji da APC da PDP, suna bukatan wanda zai tsamo su daga mawuyacin halin da kasar ke ciki."

Kara karanta wannan

Sanata Kwankwaso ya shiga Jam’iyyarsa ta 5 a tarihin siyasa bayan ya fice daga PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel