Harin jirgin kasa Abuja-Kaduna: Jerin sunayen mutum 16 da suka jikkata

Harin jirgin kasa Abuja-Kaduna: Jerin sunayen mutum 16 da suka jikkata

Kaduna - An saki jerin sunayen mutanen da suka samu rauni a harin bam da yan ta'adda suka kaiwa jirgin kasan Abuja-Kaduna ranar Litnin, 28 ga watan Maris, 2022.

A jerin sunayen da Jaridar Leadership ta wallafa akalla mutum 16:

Sun hada da Haruna Muhammed; Mohammed Modibo; Ibrahim Wakili; Yakubu Nuhu; Abdulahi Yahay; Ismail Saidu; Abdumalik Rasheedat; Umar Mohammed.

Sauran sune Hadiza Umar; Musa Ishawan; Aisha Yusuf; Mohammed Ameen; Abubakar Hauwau; Aliyu Sulaiman; Olaosebikan Bilikisu da Mrs Leola Abdulbasit.

Jerin sunayen mutum 16 da suka jikkata
Harin jirgin kasa Abuja-Kaduna: Jerin sunayen mutum 16 da suka jikkata Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC

Har yanzu ba a ji duriyar mutum dari da arba'in da shida cikin fasinjoji 362 da ke cikin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ba, kwanaki shida bayan harin da 'yan ta'adda suka kai kan jirgin.

Kara karanta wannan

Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC

Manajan daraktan hukumar kula da layin dogo ta Najeriya, Mista Fidet Okhiria ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka samo a ranar Litinin 4 ga watan Afirilu.

Rahoton Punch ya bayyana cewa, adadin fasinjojin da suka tsira ya karu zuwa 186 tun bayan harin na kwanakin nan.

Okhiria ya ce lambobin waya 51 da ke cikin takardar bayanan fasinjoji an same su a kashe ko kuma basa shiga tun da safiyar Talata yayin da lambobin waya 35 kuma suke shiga amma ba a daukar waya.

Ya kuma lura cewa lambobin waya 60 da ke cikin takardar lokacin da aka kira su, an gano babu su kwata-kwata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel