Tsige Umahi: INEC Ta Ce Ba Za Ta Bawa PDP Kejurun Gwamna Da Ƴan Majalisun 16 Ba, Ta Bada Dalilli

Tsige Umahi: INEC Ta Ce Ba Za Ta Bawa PDP Kejurun Gwamna Da Ƴan Majalisun 16 Ba, Ta Bada Dalilli

  • Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta ce ba za ta aiwatar da hukuncin kotu ta kwace kujerar Gwamna Umahi da mataimakinsa ba
  • INEC ta sanar da cewa za ta jinkirta zartar da hukuncin kotun ne domin ta samu wasu hukunce-hukuncen kotu har 12 a kan batun masu karo da juna
  • Hukumar zaben ta ce za ta saurari yadda shari'a za ta kaya a kotunan daukaka kara ko gaba da hakan kafin ta dauki mataki na karshe dangane da lamarin

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC, a ranar Alhamis ta ce ba za ta dauki wani mataki ba game da hukuncin kotu na tsige Dave Umahi a matsayin gwamnan Ebonyi bisa sauya sheka daga PDP zuwa APC a 2020.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru hudu, kotu ta saki matar da ake zargi da kisan mijinta

Hukumar ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban sashin watsa labarai da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, rahoton The Punch.

Tsige Gwamna da Kotu Ta Yi: INEC Ta Ce Ba Za Ta Dauki Mataki Yanzu Ba, Ta Bada Dalilli
Tsige Gwamna da Kotu Ta Yi: INEC Ta Ce Ba Za Ta Dauki Mataki Yanzu Ba, Ta Bada Dalilli. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Ba za mu dauki mataki ba kan tsige Umahi, mataimakinsa da yan majalisa saboda hukunce-hukuncen kotu masu karo da juna, INEC

A cewar hukumar zaben, ta samu hukunce-hukuncen kotu har guda 12 dangane da batun sauya shekar Umahi; mataimakinsa Kelechi Igwe, da yan majalisar jiha guda 16.

Don haka, INEC ta ce za ta jinkirta zartar da hukunci a kan batun saboda 'hukunce-hukuncen kotu masu cin karo da juna a kan lamarin.'

Idan za a iya tunawa, Babban kotun tarayya da ke Abuja ta tsige Umahi da mataimakinsa da yan majalisar jiha saboda sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan

Ban Damu Da Tsige Ni Da Kotu Ta Yi Ba Ko Kaɗan, Har Ƙiba Da Kyau Na Ƙara, Gwamna Umahi

Kotun ta kuma bada umurnin INEC ta maye gurbinsu da wasu mambobin jam'iyyar PDP.

Umahi ya garzaya kotu domin dakatar da tsige shi amma aka yi watsi da karar. Sai dai, kotun ta mika korafinsa ga kotun daukaka kara.

Wani sashi cikin sanarwa da INEC ta fitar a ranar Juma'a na cewa:

"Idan za a tunawa hukumar ta yi taro a ranar 17 ga watan Maris kan lamarin, ta yanke shawarar bawa sashin shari'arta damar su yi nazari su kuma bawa hukumar shawarar da ya dace.
"Tun lokacin, an gabatarwa hukumar wasu karin umurni daga kotu a kan lamarin, yanzu har guda 12. Hukumar ta yi nazari mai zurfi kansu ta kuma yanke hukuncin jinkirta daukan mataki kan sauya shekan gwamnan, mataimakinsa da yan majalisa 16 da suka fice daga PDP zuwa APC saboda umurnin kotu masu karo da juna kan batun.
"Hukumar tana ganin abin da ya fi dacewa shine jinkirta daukan wani mataki kan batun duba da umurnin da wasu kotunan daukaka kara suka bada na cewa a jinkirta daukan mataki."

Kara karanta wannan

Dan kuka: Mata za ta share harabar makarantar su danta na tsawon watanni 6 bisa laifin jibgar malami

2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC

A wani rahoton kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.

Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel