'Yan ta'adda sun sace mutum 75 a samamen da suka kai kauyukan Zamfara

'Yan ta'adda sun sace mutum 75 a samamen da suka kai kauyukan Zamfara

  • 'Yan ta'adda sun kai samame yankin Kekun Waje da ke karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara inda suka sace mutum 15
  • A kwanakin baya, miyagun sun kai farmaki inda suka sace wasu mutum sittin, lamarin da ya kai jimillar mutane 75 a hannun miyagun
  • Jama'ar yankin sun sanar da cewa 'yan bindigan sun sanar da su cewa ba za su daina kai farmaki ba har sai 'yan sa kai sun ajiye makamai

Zamfara - 'Yan ta'adda da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace a kalla mutum 75 a yankin Kekun Waje ta karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.

A wani samame da miyagun suka kai sama da wata daya da ya gabata, sun yi garkuwa da sama da mutum 60.

Kara karanta wannan

Ta hadu da bacin rana: An kama wata gurguwar karya tana bara, an tursasa ta yin tafiya a bidiyo

'Yan ta'adda sun sace mutum 75 a samamen da suka kai kauyukan Zamfara
'Yan ta'adda sun sace mutum 75 a samamen da suka kai kauyukan Zamfara. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Wadanda aka sace a wancan lokacin har yanzu suna hannun miyagun, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Mazauna yankin sun sanar da cewa miyagun na cigaba da kai farmaki daban-daban yankin bayan 'yan sa kai sun sanya musu ido.

"'Yan sa kai ne ke kare yankin. 'Yan ta'addan sun ja kunne cewa har sai 'yan ta'addan sun ajiye makamansu sannan za su sako wadanda suka kama. Da wannan sace mutum 15 din, akwai sama da mutane 76 a hannun miyagun da suka hada da mata tare da kananan yara.
"Sun yi garkuwa da mutum 61 ba a yi wata daya ba, yanzu kuma sun dawo sun sake sace wasu mutum 15. Suna bukatar 'yan sa kai su ajiye makamansu kafin su sako jama'a. Amma 'yan sa kan sun sanar da su kai tsaye cewa ba za su ajiye makamansu ba kuma za su cigaba da bai wa yankin lafiya," wani mazaunin yankin mai suna Sadiq yace.

Kara karanta wannan

Neja: 'Yan Ta'adda Sun Farmaki Kasuwa, Sun Yi Kisa, Sun Sace Mutane Da Kayan Abinci Masu Yawa

"Mun koyi darasi daga wasu yankunan masu kusanci da nan da suka shiga sasanci da 'yan ta'addan. Duk da sasancin, miyagun na cigaba da kai musu farmaki kuma suna tozarta matansu."
"Wadannan 'yan ta'addan azzalumai ne. Babu wata yarjejeniya da za a yi dasu da za su mutunta. Za su cigaba da cin zarafinmu wanda hakan yasa muka tsaya tsayin daka cewa za mu kare yankin mu duk da barazanar kawo farmaki da suke yi," ya kara da cewa.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan yankin, SP Muhammad Shehu, bai samu damar yin tsokaci a kan lamarin ha saboda ba a same shi a waya ba kafin rubuta wannan rahoton, Daily Trust ta ruwaito.

'Yan bindiga sun kwashe mutum 11 a Katsina bayan sojoji sun tattara komatsansu

A wani labari na daban, bayan janye dakarun sojoji daga kauyen Shimfida a karamar hukumar Jibiya na jihar Katsina, 'yan bindiga sun yi awon gaba da mazauna yankin guda bakwai.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Mutane 14 a Masallaci a Kaduna, Sun Kuma Bi Gida-Gida Sun Sace Mata Da Dabobbi

Premium Times ta ruwaito yadda yara bakwai suka rasa rayukan a lokacin da suka yi kokarin yin hijira daga yankin bayan janye dakarun sojojin.

An aje sojojin a makarantar sakandirin gwamnati ta Shimfida, kimanin kilomita 27 daga cikin garin Jibiya, hedkwatar karamar hukuma, har zuwa ranar Alhamis din da aka janye su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel