Jigawa: Hukumar Hisbah ta kama maza da mata 61 da ake zargi da aikata masha'a

Jigawa: Hukumar Hisbah ta kama maza da mata 61 da ake zargi da aikata masha'a

  • Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta kama wasu mutanen da ake zargi da aikata lalata a gidan magajiya
  • An kama mata 44 da ake zargin 'yan gidan magajiya ne, yayin da aka kama wasu maza 17 da sanyin safiya
  • Hukumar Hisbah ta yabawa mazauna jihar tare da gargadin mazauna kan shiga munanan ayyuka

Gujungu, Jigawa - Hukumar Hisbah a jihar Jigawa ta runtuma kame a gidan magajiya, ta kama wasu mutane 61 da suka hada da mata 44 a karamar hukumar Taura bisa zargin aikata lalata, Punch ta ruwaito.

Hukumar Hisbah dai ta yi kaurin suna wajen kama masu aikata ayyukan da suka saba da tarbiyya da al'adar malam bahaushe a Arewacin Najeriya.

Malam Ibrahim Dahiru, Kwamandan Hisbah a jihar ne ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Dutse ranar Talata 15 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Ku barmu mu tara gashi: Shehu Sani ya kai ziyara ofishin Hisbah, ya mika bukatarsa

Kamen 'yan hsibah a jigawa
Masha'a a Jigawa: Hukumar Hisbah ta kama maza da mata 44 da ake zargi da aikata lalata | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya kara da cewa jami’an Hisbah tare da hadin gwiwar ‘yan sanda ne suka kama wadanda ake zargin a ranar Litinin a babban garin ‘Gujungu’.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Matan 44 ana zargin 'yan gidan magajiya ne. Mazan 17, an kama su ne a lokacin da ‘yan Hisbah suka kai farmaki yankin da misalin karfe 6 na safe.
“An riga an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban wata kotun majistare da ke Ringim.”

Dahiru ya bukaci mazauna jihar musamman matasa da su daina aikata munanan dabi’u da za su iya lalata makomarsu sannan su jajirce wajen inganta rayuwar al’umma.

Ya kuma yabawa mazauna jihar bisa goyon bayan da suke baiwa hukumar domin samun damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

A cewarsa, hukumar ta Hisbah za ta ci gaba da yaki da munanan dabi’u a duk sassan jihar.

Kara karanta wannan

Jerin yadda Sojoji 18, yan sanda 6 da yan Najeriya 76 suka rasa rayukansu cikin mako daya

'Yan Hisbah sun kama mutum 47 suna sheƙe ayansu, ciki har da mata 16, an ƙwace kwallaban giya 745

Hukumar Hisbah reshen jihar ta kama mutane 47 da ake zargin su na aikata rashin da’a ciki har da mata 16 kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kwamandan rundunar ta jihar, Malam Ibrahim Dahiru ne ya tabbatar da kamen ta wata hira da menama labarai su ka yi da shi jiya a Dutse, babban birnin jihar.

Bisa ruwayar jaridar The Nation, Dahiru ya ce a cikin wadanda aka kama har da wadanda ake zargin karuwai ne su 16.

Kuma an kama su ne bayan kai samamen da hukumar ta yi a gidajen giya, gidajen karuwai da sauran wuraren da mutanen banza ke zama.

Ya ce sun zagaye kananun hukumomi 11 da ke cikin jihar.

Ku barmu mu tara gashi: Shehu Sani ya kai ziyara ofishin Hisbah, ya mika bukatarsa

Kara karanta wannan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

A wani labarin, dan siyasa kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Sanata Shehu Sani a ranar Litinin, 14 ga watan Maris ya ziyarci shahararriyar hukumar Hisbah ta jihar Kano.

Da yake zantawa da manema labarai kan ziyarar, Sanata Sani ya ce ya je ofishin hukumar ne domin neman bayani kan wasu abubuwa da kuma sanin ayyukan Hisbah biyo bayan cin karo da ya yi da labarai da dama da ake danganta su da hukumar a fadin jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi yana cewa:

“An fadi abubuwa da yawa game da Hisbah kuma na yi imanin cewa a matsayina na tsohon Sanata, mai fafutukar kare hakkin bil’adama da na jama’a, a zahiri ya kamata in ziyarci ofishinsu na ji ta bakinsu inji wane irin aiki suke yi da nauyin da ya rataya a wuyansu da kuma batutuwan da ake danganta su da su."

Kara karanta wannan

NIS ta kama ma’aikata ‘yan China sama da 200 a Neja ba su da biza, wasu sun tsere

Asali: Legit.ng

Online view pixel