Yajin Aikin ASUU: BUK Ta Umarci Duk Ɗaliban Da Ke Zama a Makaranta Su Kwashe Ya-Nasu Ya-Nasu Su Tafi Gida

Yajin Aikin ASUU: BUK Ta Umarci Duk Ɗaliban Da Ke Zama a Makaranta Su Kwashe Ya-Nasu Ya-Nasu Su Tafi Gida

  • Jami’ar Bayero da ke Kano, BUK, ta umarci duk daliban da ke zama a cikin makarantar da su kwashe kayan su, su bar dakunan da suke zama zuwa ranar 20 ga watan Maris
  • Har ila yau, jami’ar ta dakatar da duk wasu ayyuka da ake gudanarwa a makarantar har sai an dawo daga yajin aikin ASUU da aka tafi
  • An samu wannan bayanin ne ta wata takarda wacce sakataren watsa labaran jami’ar, Bala Abdullahi ya saki a maimakon magatakardar jami’ar

Kano - Jami’ar Bayero da ke Kano, BUK ta umarci duk wasu dalibai da ke zama a cikin rassan makarantar guda biyu akan su kwashe ya-nasu ya-nasu su bar harabar makarantar zuwa ranar 20 ga watan Maris ko kafin nan.

Yajin Aikin ASUU: BUK Ta Umarci Duk Daliban da Ke Zama a Makaranta Su Kwashe Ya-Nasu Ya-Nasu Su Tafi Gida
Yajin Aikin ASUU: BUK Ta Umarci Duk Daliban da Ke Zama a Makaranta Su Kwashe Ya-Nasu Ya-Nasu. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Sannan jami’ar ta dakatar da duk wasu ayyukan da ake yi cikin jami’ar har sai makarantar ta dawo daga yajin aikin gaba daya, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

PDP ta tausayawa matasa wajen biyan kudin fam din takara, ta rage masu 50% da wasu hukunci 11 da ta zartar

A wata takarda wacce sakataren watsa labaran jami’ar, Bala Abdullahi ya saki a maimakon magatakardar jami’ar, inda ya kula da cewa wannan matakin ya biyo bayan kara watanni 2 da ASUU ta yi na yajin aikin ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba BUK ce kadai ce jami’ar da ta dauki wannan matakin ba

Kamar yadda takardar ta zo:

“Hukumar makarantar za ta dakatar da duk wasu ayyukan da ke wakana a cikin rukunin dakunan daliban.”

Daily Trust ta ruwaito yadda a ranar Alhamis jami’ar Ibadan (UI) ta rufe makarantar har sai kaka ta gani, don haka ta umarci duk daliban jami’ar su kwashe komai na su take yanke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel