Ka yi murabus yanzun, ka mika mulki ga Osinbajo, Gwamnan PDP ga Buhari

Ka yi murabus yanzun, ka mika mulki ga Osinbajo, Gwamnan PDP ga Buhari

  • Gwamnan jihar Benuwai ya koka kan taɓarɓarewa matsalar tsaro a jiharsa, ya nemi shugaba Buhari ya yi murabus
  • Samuel Ortom ya ce Buhari ya gaza ta kowane bangare na alkawurran da ya yi wa yan Najeriya dan haka ya mika mulki ga Osinbajo
  • Ya kuma umarci al'ummar jiharsa su ɗauki makamin da doka ta amince su kare kan su daga sharrin baragurbin fulani

Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ranar Litinin, ya yi kira ga shugaban ƙasa, Muhammadu, Buhari ya gaggauta yin murabus, ya damƙa mulki hannun mataimakinsa, Yemi Osinbajo.

Gwamna Ortom ya yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai da ya gudana a Makurɗi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yace shugaban ƙasa Buhari ya kunyata yan Najeriya a kowane alkawari da ya ɗauka lokacin zabe, musamman ƙara taɓarɓarewa matsalar tsaro a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Matar Abba Kyari ta yanke jiki ta fadi a cikin kotu

Gwamna Samuel Ortom
Ka yi murabus yanzun, ka mika mulki ga Osinbajo, Gwamnan PDP ga Buhari Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ortom na ɗaya daga cikin yan gaba-gaba wajen sukar gwamnatin shugaba Buhari musamman a abin da ya shafi tsaro da tattalin arzikin ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Ortom ya ce:

"Gwamnatin tarayya ta gaza baki ɗaya, kuma ina kira ga shugaba Buhari ya amince ya kunyata Najeriya kuma ina shawartarsa ya yi murabus daga matsayin shugaban ƙasa."
"Kwarai kuwa, ya aje mukaminsa ma miƙa mulki ga mataimakinsa ya cigaba da tafiyar da harkokin ƙasa, idan ba haka ba kullun Najeriya ƙara ci baya take."

Ku ɗauki makami ku kare kan ku - Ortom ga mutanen jiharsa

Gwamnan ya koka da ƙarin ƙashe-kashen da ake samu a ƙaramar hukumarsa Guma da sauran sassan jihar Benuwai, wanda ake zargin bara gurbin Fulani da aikata wa.

Ya ce babu dalilin da zaisa mutane su yi ta ɓannatar da hawayen su wajen neman a kawo musu ɗauki tun da ba wani mataki da gwamnatin tarayya ke ɗauka na kawo karshen al'amarin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Shugaba Buhari ya yi magana kan rikicin APC, ya gargaɗi wasu mutane

Ya kuma ƙara da cewa mutanensa sun shirya ɗaukar makami kamar yadda doka ta tanadar domin su kare kansu.

"Zan ɗauki matakin da ya dace, na yi shawari da mutane na kuma na yanke abinda zan yi, ba zan faɗa kowa ya ji ba. Za mu ɗauki tsattsauran mataki domin an kai mu bango."

A wani labarin kuma Gwamna Matawalle ya gargaɗi gwamnoni abu daya game da rikicin shugabancin APC

Gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya gargaɗi gwamnonin APC kan kalaman wuce gona da iri game da rikicin cikin gida.

Gwamnan ya ce kowane daga cikinsu na taka rawa wajen cigaban APC, kuma haka gwamna Buni, ya yi matukar kokari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel