Dokar zabe: Tashin hankali yayin da majalisa ta yi watsi da dokar zabe ta Buhari

Dokar zabe: Tashin hankali yayin da majalisa ta yi watsi da dokar zabe ta Buhari

  • Majalisar Dattawa ta yi watsi da kudurin dokar zabe da shugaba Buhari ya gabatar saboda wasu dalilai
  • A baya majalisar ta fusata da jin yadda kotu ta ba da umarni gareta cewa, kada ta sake ta gyara dokar zaben
  • A yau dai majalisar ta kawo karshen magana, ta kada kuri'a kuma an yi watsi da dokar gabanin karatu na biyu

FCT, Abuja - Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, majalisar dattawa a ranar Laraba ta yi watsi da kudirin doka da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar na neman gyara dokar zabe ta 2022.

Kudirin doka mai taken: “Kudirin dokar da zai gyara dokar zabe ta 2022 da kuma abubuwa masu alaka, 2022,” Sanatoci sun yi watsi da shi, lamarin da ya dakatar da karatun kudurin na biyu.

Kara karanta wannan

Tafiyar Buhari Landan: Har yanzu shuru, Buhari bai sanar da Majalisa ya mika mulki ga Osinbajo ba

Kudurin dokar ya tsallake karatu na farko a ranar Talata duk da umarnin da kotu ta bayar na hana Majalisar Dattawa yin aiki akansa.

Majalisa ta yi watsi da kudurin dokar zabe ta Buhari
Yanzu-Yanzu: Majalisa ta yi waje da bukatar Buhari ta gyara kudurin zabe | Hoto: channelstv.com
Asali: Twitter

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya kalubalanci hukuncin kotun yana mai cewa a kowane hali, bangaren shari’a bai da ikon hana majalisar gudanar da ayyukanta na tsarin mulki.

Kafin Majalisar Dattawa ta fara nazarin kudirin a ranar Laraba, Sanata Adamu Aliero, yayin da yake karanto doka ta 52 (5) na Majalisar Dattawa, ya bukaci Shugaban Majalisar da ya yi watsi da shawarar duba ga kudirin.

Sai dai Lawan ya dage. Ya sake jaddada matsayinsa na cewa Sanatoci ne ke da hakkin kin amincewa da kudirin ba bangaren shari’a da ke neman hana majalisar gudanar da ayyukanta ba.

Saboda haka, Sanatoci sun kada kuri'ar kin amincewa da kudirin na hana sake karanta shi a karo na biyu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bayelsa ya yabi Buhari, ya ce Shugaban kasa ya ba ‘Yan Najeriya ‘kyauta’

Bukatar shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta yi wa sashe na 84 (2) karamin sashe na 12 da ke cewa babu wani mai rike da mukamin siyasa da zai zama wakilin zabe ko kuma a zabe shi a taron gangamin wata jam’iyyar siyasa da nufin tsayar da kowane dan takara.

Shugaba Buhari ya nemi gyaran ne bayan rattaba hannu kan kudurin, lamarin da ya kai ga batun gaba wata kotu a kasar nan, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Shugaban majalisar dattawa ya ce sam kotu ba ta da hurumin hana majalisa rattaba hannu kan wata doka, don haka ba za ta hanu daga aikinta ba.

Legit.ng Hausa ta tuntubi wani kwararren lauya, Ibrahim Ahmad Kala Esq. wanda ya tabbatar da cewa:

"Majalisa ce ke da damar sauya doka ko gyara ta ko kuma yi mata kwaskwarima, don haka kotu tana iya amfani ne da kudin da majalisa ta amince dashi ne.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi saboda kokarin Buhari

"Saboda haka, Ahmad Lawan na da gaskiya, kotu ba ta da hurumin hanawa ko saka majalisa ta sa hannun kan wani kuduri."

Shugaba Buhari ya bada umurnin cire Buni, ya so ya ha'ince mu: El-Rufai

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ba zai taba komawa kujerar Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana hakan.

A hirar da yayi a shirin Politics Today, El-Rufa'i ya ce Buni ko ya dawo an fitittikeshi daga kujerar gaba daya har abada.

Ya ce Shugaba Buhari da gwamnonin APC 19 sun yi ittifaki kan cire Mai Mala Buni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel