'Karin Bayani: Wani Bam Ya Sake Fashewa a Kauyen Jihar Niger

'Karin Bayani: Wani Bam Ya Sake Fashewa a Kauyen Jihar Niger

Jihar Niger - An sake samun fashewar sabuwar bam a garin Galadima-Kogo, karamar hukumar Shiroro a Jihar Niger.

Daily Trust ta rahoto cewa bam din ya fashe ne misalin karfe 7 na daren ranar Juma'a.

Labari Da Duminsa: Wani bam ya sake fashewa a Jihar Niger
Labari Da Duminsa: Wani bam ya sake fashewa a Jihar Niger
Asali: Original

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan jihar Niger, DSP Wasiu Abiodun ya yi alkawarin zai yi bincike ya sake kira amma bai a ji daga gare shi ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

An yi kokarin ji ta bakin kwamishinan kananan hukumomi da masarautu da cigaban unguwanni da tsaron cikin gida, Emmanuel Umar, amma ba a same shi ba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotu ta yiwa kasurgumin mai garkuwa da mutane, Evans, hukuncin daurin rai da rai

Shugaban kungiyar matasan Shiroro ya tabbatar da fashewar bam din

Sani Abubakar Yusuf Kokki, daya cikin wadanda suka kafa kungiyar matasa na Shiroro ya ce:

"Wani abin fashe wa da ake kyautata zaton bam ne ya fashe a Galadima Kogo, a karamar hukumar Shiroro, Jihar Niger."

Hakan na zuwa ne kasa da kwanaki biyar bayan wani bam ya tashi a garin, ya kashe jami'an hukumar tsaro da NSCDC guda hudu.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel