Zulum Ya Gwangwaje Tubabbun 'Yan Daba Su 152 Da Naira Miliyan 100 A Borno

Zulum Ya Gwangwaje Tubabbun 'Yan Daba Su 152 Da Naira Miliyan 100 A Borno

  • Babagana Zulum, gwamnan Jihar Borno ya bai wa tubabbun yan daba su 152 tallafin kudi Naira miliyan 100 su ja jari bayan koyar da su sana'a
  • Har wa yau, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta dauki nauyin karatun mutum daya daga gidajen dukkanin wadanda suka samu tallafin
  • Gwamnan na Borno ya ce ana sa ran wadanda aka bai wa tallafin don jan jari za su dawo da kashi 50 cikin 100 na kudin bayan shekara uku

Jihar Borno - Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno, a ranar Juma'a, ya raba wa matasa 152 da suka tuba da dabanci Naira miliyan 100, domin su ja jari su fara sana'a, Daily Nigerian ta ruwaito.

Zulum, wanda ya kaddamar da shirin a Maiduguri, ya ce an bada tallafin ne ga matasan da aka yi wa horaswa na wata daya domin su fara sana'a da zai amfani jihar da tattalin arzikinta.

Kara karanta wannan

Ku mika wuya tun kafin mu iso maɓoyarku, Sabon Kwamishina ya aike da sako ga yan bindiga

Zulum Ya Gwangwaje Tubabbun ’Yan Daba Su 152 Da Naira Miliyan 100 a Borno
Zulum Ya Ba Wa Tubabbun ’Yan Daba Su 152 Da Naira Miliyan 100 a Borno. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Twitter

Ya ce mutum 16 cikin wadanda za su amfana da tallafin za su samu N2m kowannensu yayin da saura 136 za su samu 500,000 kowannensu.

A cewarsa, ana sa ran wadanda aka bawa tallafin su biya kashi 50 cikin 100 na kudin da aka ba su bayan shekaru uku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya kuma sanar da cewa gwamnatin jiharsa za ta dauki dawainiyar karatun yaro daya daga gidajen dukkan wadanda suka amfana da tallafin.

Ya ce:

"Kun yi dabanci na tsawon shekaru amma bai amfane ku da komai ba, da abin da muka baku, idan kuna da niyya mai kyau da shirin canja wa, za ku canja ku zama mutanen kirki."

An koyar da matasan kiwon tumaki, kifi, kaji da ilimin sana'a da kasuwancin intanet

A jawabinsa, Dr Mustapha Muhammad, Shugaban sashin koyar da sana'a, Ramat Polytechnic Maiduguri, ya ce an koyar da matasan sana'o'i kamar kiwon dabobi, kiwon kifi, kiwon kaji, ilimin sana'a da kasuwanci na yanar gizo.

Kara karanta wannan

Ni ba zan kore ku ba: Gwamna Zulum ya gano Malamai 3800 ba su da abinci a koyarwa

Daya daga cikin wadanda suka amfana da abin, Tijjani Daga, ya yaba wa karamcin ya kuma yi alkawarin za su yi amfani da kudin domin inganta rayuwansu.

Ya ce:

"Muna godiya ga gwamnan bisa tallafin, kuma daga yau ba za mu sake koma wa dabanci ba."

Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023

A wani rahoton, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.

Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel