An samu Jami’ar Najeriya da ta juyawa 'Yan ASUU baya, ta ce ba za ta shiga yajin-aiki ba

An samu Jami’ar Najeriya da ta juyawa 'Yan ASUU baya, ta ce ba za ta shiga yajin-aiki ba

  • Jami’ar Chukuwuemeka Odumegwu Ojukwu ta nesanta kanta da yajin-aikin da malamai suka shiga
  • Shugaban kungiyar Progressive Academic Staff Union of Universities ya ce ba za su tafi yajin-aiki ba
  • Farfesa Osita Chiaghanam ya bayyana cewa ba za su yi abin da ba zai taimaka wajen kawo cigaba ba

Anambra - Shugaban wata kungiya, Progressive Academic Staff Union of Universities, Farfesa Osita Chiaghanam ya yi watsi da yajin-aikin da ASUU ta shiga.

A ranar Talata, 15 ga watan Fubrairu 2022, jaridar Vanguard ta rahoto Farfesa Osita Chiaghanam yana cewa babu ruwan jami’arsu da wannan yajin-aiki da ake yi.

Da ya zanta da manema labarai, shugaban kungiyar ya ce jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu ba za tayi abin da ba zai taimaka wajen kawo cigaba ba.

Kara karanta wannan

Farfesancin Dakta Pantami: Jami'ar FUTO ta fusata, ta ce ta maka ASUU a kotu

A cewar Farfesan, babbar manufar wannan jami’a ita ce yara su samu ilmi ba tare da bata lokaci ba.

Chiaghanam ya shaidawa hukumar dillacin labarai a garin Awka cewa kungiyarsu ta Progressive Academic Staff Union of Universities za ta bunkasa harkar ilmi.

Jami’ar Najeriya
Jami’ar Chukuwuemeka Odumegwu Ojukwu a Anambra Hoto: coou.edu.ng
Asali: UGC

“Mun dage wajen ganin mun maida makarantarmu ta zama cibiyar ilmi. Za mu yi kokarin kawowa makarantar cigaba ta lalama, ba tare da tsaida karatu ba.”
“Ba za mu biyewa wata kungiya ko daidaikun mutane wajen shiga yajin-aikin da ba zai amfani kowa a jami’ar Chukuwuemeka Odumegwu Ojukwu ba.”

- Farfesa Osita Chiaghanam

Kishiyar ASUU?

Jaridar Tribune ta rahoto Chiaghanam yana cewa kungiyarsu ba ta da matsala da ‘Yan ASUU.

Shugaban wannan kungiya da ake ganin tana yin adawa da ASUU ya jero nasarorin da jami’arsu ta samu a karkashin jagorancin shugabanta, Farfesa Greg Nwokoby.

Kara karanta wannan

ASUU za tayi zamanta na karshe yau, gobe za ta yanke shawara kan yajin aiki

A matsayinsa na shugaban jami’a, Farfesa Nwokoby ya biya ma’aikata hakkokinsu, ya gina sakatariyar ASUU, Chiaghanam ya ce ba za su daina zuwa ofis ba.

Malamin jami’ar ya ce kafin yanzu ba a san jami’o’in jiha da biyewa makarantun tarayya wajen tafiya yajin-aiki ba, don haka zai fi kyau su zauna da gwamnoninsu.

NANS ta soki FG, ASUU

A makon nan aka ji labari kungiyar daliban Najeriya, ta yi Allah-wadai da sabon yajin-aikin da malaman jami’a su ka sake tafiya bayan shekara daya da dawowa aiki.

Shugaban kungiyar NANS na kasa, Asefon Sunday ya fitar da jawabi, yana kokawa a kan wannan yajin-aikin. NANS ta ce za ta shirya zanga-zanga domin nuna fushinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel